Afcon 2025: Super Eagles ta kasa cin Rwanda a Kigali

Super Eagles

Asalin hoton, The NFF

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Tawagar ƙwallon kafa ta Najeriya ta je ta tashi ba ci 0-0 da Rwanda a wasa na biyu a neman shiga gasar kofin Afirka da za a yi a Morocco a 2025.

Super Eagles ce ta mamaye wasan, amma ta kasa zura ƙwallo a raga duk da damar makin da ta samu a karawar da suka yi a birnin Kigali a Rwanda.

Najeriya ta kai hare-hare 20 a fafatawar, amma tara ne suka nufi raga kai tsaye, inda Rwanda ta kai hari 16, biyu daga ciki suka nufi raga.

Super Eagles ta yi laifi 16, Rwanda kuwa 14, yayin da Najeriya ta yi kwana 7, ita kuwa Rwanda ta yi uku, an kuma raba katin gargaɗi huɗu, kowacce ta karɓi biyu.

Da wannan sakamakon Super Eagles tana ta ɗaya a kan teburin rukuni na huɗu da maki huɗu a wasa biyu.

Ita kuwa Rwanda maki biyu ne da ita a karawa biyu, sakamakon da ta tashi 1-1 da Libya ranar Laraba 4 ga watan Satumba.

Ita kuwa Najeriya ta doke Benin 3-0 ranar Asabar 7 ga watan Satumba a birnin Uyo a jihar Akwa Ibom a Najeriya.

idan an jima za a buga ɗaya wasan rukuni na huɗun tsakanin Benin da Libya.

Sai a cikin watan Oktoba za a ci gaba da wasa na uku-uku a cikin rukuni, inda Super Eagles za ta karɓi bakuncin Libya da wanda Rwanda za ta ziyarci Benin.

Najeriya da Rwanda da Benin suka rukuni na uku a wasannin neman shiga gasar kofin duniya da za a yi a Amurka da Canada da Mexico a 2026.

Rwanda ce ta ɗaya a rukunin da maki bakwai, iri daya da na Afirka ta Kudu da Benin.

Lesotho ce ta huɗu da maki biyar da Super Eagles ta biyar mai maki uku da kuma Zimbabwe ta karshe da maki biyu.