Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Fitattun ƴan ƙwallon ƙafar duniya da asalinsu ƴan Najeriya ne
Magoya bayan tawagar ƙwallon ƙafa ta Najeriya sun daɗe suna nuna rashin jin daɗinsu kan tawagar, kan yadda take gaza taka rawar gani a gasanni ko dai na nahiyar Afirka ko ma a matakin duniya.
Tawagar Super Eagles ta ja zare a shekarun baya, inda ake yi wa tawagar kallon babba kuma mafi ƙwazo a nahiyar Afirka, musamman bayan lashe gasar Olympic da aka yi a Atalanta a 1996, inda ƙasar ta doke Brazil da Argentina.
Sai dai daga bisani harkokin taka leda da tawagar ke yi ya samu koma-baya, inda wasu tawagogin nahiyar suka fara nuna mata yatsa.
A lokuta da dama, akan ɗora laifin rashin nasarar tawagar ƙasar a kan ƴan wasan, inda wasu ke ganin suna nuna ƙwarewa a ƙungiyoyinsu na Turai, amma da zarar sun koma gida, sai su zama tamkar ba su ba.
Najeriya na cikin ƙasashen duniya da suke da zaratan ƴan ƙwallo da suke nuna bajinta a tamaula a Turai.
Amma duk da haka akwai wasu zaratan ƴan ƙwallo da asalinsu ƴan ƙasar ne, amma suke wakiltar wasu ƙasashen daban.
Wannan ya sa BBC ta zaƙulo wasu zaratan ƴan ƙwallo da tauraronsu ke haskawa a duniya, waɗanda asalin ƴan Najeriya ne, wato ko dai iyayensu baki ɗaya ko wani daga cikin iyayen ƴan Najeriya ne.
Jamal Musiala
Jamal Musiala, wanda aka haifa a ranar 26 ga Fabrairun shekarar 2003, fitaccen ɗan ƙwallon ƙasar Jamus ne da ƙungiyar Bayern Munich ta Jamus ɗin kuma yana cikin matasan ƴan ƙwallon da suke tashe a duniya a yanzu.
An haife shi ne a garin Stuttgart da ke Jamus, amma mahaifinsa mai suna Daniel Richard asalin ɗan Najeriya ne, wanda ya yake da shaidar zama ɗan Ingila, mahaifiyarsa mai suna Carolina kuma ƴar Jamus ce.
Ya wakilci ƙasar Ingila a ƙwallon matakin yara, kafin ya koma Jamus da taka leda.
Ya lashe kofuna da dama irin su gasar Bundesliga guda huɗu da sauran kofuna, sannan ya samu kyaututtuka da dama.
Karim Adeyemi
Karim-David Adeyemi wanda aka haifa a ranar 18 ga watan Janairun shekarar 2002, ɗan wasan Jamus ne da ƙungiyar Dortmund.
An haifi ɗan wasan a birnin Munich, wanda mahaifinsa asalin ɗan Najeriya, amma mahaifiyarsa ƴar Romaniya ne .
A kwanakin baya ɗanwasan da ke taka leda a Dortmund da ke Jamus. A baya-bayan nan Karim Adeyemi ya buɗe wata gidauniya a Najeriya.
Ya buɗe gidauniyar ne a birnin Ibadan da ke jiyar Oyo a kudu maso yammacin Najeriya, inda ya ce gidauniyar za ta mayar da hankali kan koyar da wasanni da ilimi.
A lokacin da ya ziyarci Najeriya, Adeyemi ya shaida wa BBC cewa nan gaba yana tunanin komawa taka leda a gasar Premier ta Ingila.
Michael Olise
An haifi Michael Akpovie Olise, a ranar 12 ga Disamban 2001, ɗan ƙwallo da a yanzu yake wakiltar Faransa kuma yake taka leda a ƙungiyar Bayern Munich.
Asalin mahaifinsa ɗan Najeriya, amma mahaifiyarsa ƴar Aljeriya ce mazauniyar Faransa.
Noni Madueke
Asalin sunansa Chukwunonso Tristan "Noni" Madueke, kuma an haife shi ne a ranar 10 ga Maris a shekarar 2002.
Yanzu yana wakiltar ƙasar Ingila ne, sannan yana taka leda a ƙungiyar Chelsea ta Ingila.
Asalin mahaifinsa ɗan Najeriya, amma shi a Ingila aka haife shi.
Bukayo Saka
Bukayo Saka fitaccen ɗanƙwallo ne da a yanzu yake jan zarensa a ƙungiyar Arsenal ta Ingila.
Ɗanwasan wanda asalin sunansa Bukayo Ayoyinka Temidayo Saka, iyayensa Adenike da Yomi Saka duka ƴan Najeriya ne.
Sai dai ya sha bayyana cewa yana alfahari da kasancewarsa ɗan Najeriya, kuma yakan ziraci ƙasar.
Ethan Chidiebere Nwaneri
Ethan Chidiebere Nwaneri wanda aka haifa a ranar 21 ga watan Maris na 2007, matashin ɗanwasa ne da a yanzu yake tashe a ƙungiyar Arsenal.
An haife shi ne a arewacin Landan, amma iyayensa ƴan Najeriya.
Ya wakilta tawagar ƴanwasan ƙasa da shekarab 16 da 17 da 19.
Har yanzu ba wakilci babbar tawagar Ingila ba, wanda hakan ya sa za a iya gayyatarsa Najeriya.
Joshua Orobosa Zirkzee
Joshua Orobosa Zirkzee wanda aka haifa a ranar 22 ga Mayun 2001, ɗan ƙwallo ne da yake wakiltar ƙasar Netherlands, kuma yake taka leda a ƙungiyar Manchester United ta Ingila.
An haife shi ne a birnin Schiedam, sai dai shi mahaifiyarsa ce ƴar Najeriya, amma mahaifinsa ɗan Netherland ne.