Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Waiwaye: Shirin sauya ministoci da ƙara wa masu yi wa ƙasa hidima alawus
Wannan maƙale ce da ke kawo muku muhimman batutuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi.
Nan gaba kaɗan Tinubu zai sauya wasu ministoci - Fadar shugaban ƙasa
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana cewa zai yi wa majalisar ministocinsa kwaskwarima nan gaba kaɗan, kamar yadda mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya sanar.
"Shugaban ƙasa ya ce zai yi wa majalisarsa kwaskwarima. Ban sani ba ko zai yi hakan kafin 1 ga watan Oktoba amma dai tabbas zai yi.... bai dai faɗa mana lokaci ba, amma tabbas zai yi" in ji Onanuga.
Mista Onanuga ya ce shugaban ya kuma umarci ministoci "da su daina jin kunyar yin magana da kafofin yaɗa labarai" domin tallata ayyukan gwamnatin.
A cewarsa "wasu daga cikinsu na gudun magana a talabijin, ko rediyo. Ya nemi su daina yin hakan, su fita su bayyana ayyukan da suke yi."
Gwamnatin Najeriya ta ƙara wa masu yi wa ƙasa hidima alawus zuwa N77,000
Gwamnatin Najeriya ta amince ta ƙara alawus ɗin masu yi wa ƙasa hidima daga naira 33,000 zuwa naira 77,000, wanda zai fara aiki daga Yulin 2024.
An yi ƙarin alawus ɗin ne saboda ƙarin mafi ƙarancin albashi da gwamnatin Najeriya ta yi, kamar yadda kakakin Hukumar NYSC, Caroline Embu ta bayyana a wata sanarwa.
Ta ce sun samu takarda daga Hukumar Albashi ta ƙasa wato National Salaries, Incomes and Wages Commission, wadda shugabanta Ekpo Nta ya saka wa hannu a ranar 25 ga Satumba domin aiwatar da ƙarin alawus ɗin.
A watan Yuli ne Majalisar Dokokin Najeriya suka amince da ƙarin mafi ƙarancin albashi zuwa naira 70,000, wanda shugaban ƙasa ya rattaba hannu.
Matakin ya yi wa masu yi wa ƙasa hidimar daɗi, kasancewar da ma sun jima suna kokawa kan buƙatar ƙara musu kuɗin alawus ɗin.
Saki da kuma korar Seaman Abbas daga aiki
A safiyar ranar Juma'a ne labarin sojan ruwan nan mai suna Seaman Abbas Haruna da mai ɗakinsa ta fallasa irin uƙubar da yake ciki tsawon shekaru shida, ya sauya bayan sojan da mai ɗakinsa sun bayyana a tashar Brekete Family.
Mai ɗakin nasa dai Hussaina cikin rawar murya da kuka ta shaida wa tashar cewa "sun kore shi. Sun fito da shi daga gate. Ko sun ɗauka ba na son mijina, Allah ya sa haka ne ya fi alkairi. Koma dai me suka yi masa ni ina son mijina."
BBC ta tambayi mai magana da yawun rundunar tsaron Najeriya, Birgediya Janar Tukur Gusau dangane da ko a wane hali aka sallami sojan.
"Ranar Alhamis aka sake shi sannan kuma an kore shi daga aiki". In ji Birgediya Janar Tukur Gusau.
Bisa al'adar aikin soji da ma sauran ayyukan gwamnati a Najeriya, idan aka kori mutum daga aiki to ba za a ba shi haƙƙoƙinsa ba.
Kotun soji ce dai kawai take da hakkin korar mutum daga aikin soji a Najeriya.
PDP za ta kai ƙara kotu kan sakamakon zaɓen gwamnan Edo
Jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta ce za ta kai ƙara kotu game da sakamakon zaɓen gwamnan jihar Edo a kudu maso kudancin ƙasar da aka yi a ƙarshen mako.
A ranar Lahadin da ta gabata ne hukumar zaɓe ta ƙasa ta bayyana ɗantakarar jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya amma mai adawa a jihar, Monday Okpebholo, a matsayin wanda ya yi nasara da ƙuri'a 291,667.
Sai kuma ɗantakarar PDP mai mulkin jihar, Asuerinme Ighodalo, wanda ya zo na biyu da ƙuri’a 247, 274.
Da yake magana yayin wani taron manema labarai a Abuja babban birnin ƙasar, muƙaddashin shugaban PDP na ƙasa Umar Damagun ya nemi hukumar zaɓe ta sake duba sakamakon.
"Duk da tashin hankali, da tilastawa, da maguɗin da APC ta yi, sakamakon da muka tattara daga rumfunan zaɓe sun nuna ƙarara ɗantakararmu Ighodalo ne ya ci zaɓen kafin a sauya sakamakon a cibiyar tattarawa ta jiha," a cewarsa.
A cewarsa, matakin da kotuna suka yanke game da ƙorafin da za su shigar ne "zai tantance ko har yanzu 'yan Najeriya na alfahari da ƙasarsu ko kuma a'a".
Cibiyar Yiaga Africa da ta sa ido a zaɓen ta bayyana cewa akwai kurakurai game da sakamakon da hukumar zaɓe ta sanar da wanda aka tattara daga rumfunan zaɓen.
Ƙara kuɗin ruwa akai-akai ya taimaka wa darajar naira - Gwamnan CBN
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ce ƙarin kuɗin ruwa da dinga yi akai-akai ya taimaka wajen ƙarfafa gwiwar 'yan ƙasar game da tunaninsu kan takardun kuɗi na naira.
Gwamnan CBN Olayemi Cardoso ya ce kuma bayyana matakin bankin na sake ƙara kuɗin ruwan zuwa kashi 27.25 a yau Talata jim kaɗan bayan kammala taron kwamatin harkokin kuɗi.
Hakan na nufin duk mutumin da ya ci bashin banki yanzu sai ya biya kuɗin ruwan kashi 27.25 na kuɗin da ya karɓa. CBN na cewa yana yin hakan ne da zimmar rage hauhawar farashi.
"Mun kusa faɗawa matsalar zagayawar kuɗi tsakanin jama'a a 2017 zuwa 2023, kuma mun ga yadda aka dinga zuba kuɗi a hannun jama'a," in ji shi yana mai zargin wanda ya gada, Godwin Emefiele.
"A 2015, yawan kuɗin da ke zagayawa a hannun jama'a sun kai naira biliyan 19, a 2023 kuma tiriliyan 54. Wannan babban ƙari ne...Saboda haka buga takardun kuɗin na jawo yawan kuɗi.
"Saboda haka, mun yi imanin cewa yawan ƙara kuɗin ruwan ya taimaka wa mutane wajen sauya tunani game da takardun kuɗin, kuma yanzu akwai alfanu mai girma idan mutum yana riƙe da naira ba kamar a baya ba."
A ƙarƙashin Cardoso - wanda ya fara aiki a watan Satumban 2023 - ana canzar da dala ɗaya kan naira 1,600, saɓanin N700 da ake canzarwa a lokacin da ya kama aikin.
An kashe fitattun ƴanbindiga Kachalla Sani Black da Sharme
Rahotanni na nuna cewa an kashe ƙasurgumin ɗanbindiga, Kachalla Sani Black a Zamfara.
Ƴan sa-kai ne suka fafata da ɗanbindigar, suka kashe shi, suka ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda biyu, da wasu ƙudade.
Kafar PRNigeria ta ruwaito cewa bayan kashe ɗanbindigar, an kuma kashe ƴaƴansa biyu a fafatawar da aka yi a yankin Magama Mai Rake da ke ƙaramar hukumar Maru da ke jihar Zamfara.
Kachalla Sani Black fitaccen ɗanbindiga ne da ya addabi yankin Chabi da Ɗan Sadau a ƙaramar hukumar Maru da wasu yankuna na arewacin Zamfara da Kaduna da Neja da Kebbi.