Watakila Toney ya koma Al-Ahli, City na son Guardiola ya tsawaita kwantiraginsa

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Wakilan dan wasa mai kai hari na Brentford da Ingila Ivan Toney na tattaunawa da kungiyar Al-Ahli ta Saudi Pro League domin siyan dan wasan mai shekara 28. (Teamtalk), external

A makon daya gabata ne Brentford ta yi watsi da tayin da Al-Ahli ta yi wa Toney. (Telegraph), external

Manchester United ba ta da sha’awar daukar Toney. (Sky Germany), external

Manchester City na son kocinta Pep Guardiola, mai shekara 53, ya yanke shawara kan ko zai rattaba hannu kan sabon kwantiragi da kungiyar kafin kirsimeti. A shekarar 2025 ne kwantiragin dan kasar Sfaniya na yanzu zai zo karshe. (Sky Sports), external

Nottingham Forest da Villarreal da Sevilla, da kuma Valencia na zawarcin dan wasa mai tsaron baya na Aston Villa da Sfaniya Alex Moreno, mai shekara 31. (Football Insider), external

Panathinaikos na tattaunawa da Manchester United kan cinikin dan wasan tsakiyar Uruguay Facundo Pellistri mai shekara 22. (Athletic - subscription required), external

Atletico Madrid ba ta yanke shawara a kan ko za ta sayi dan wasan tsakiya na Valencia da Sfaniya Javi Guerra mai shekara 21 yayin da yarjejeniyar da su ke son su kulla da dan wasa tsakiya na Chelsea da Ingila Conor Gallagher mai shekara 24 ya gamu da cikas. (Athletic - subscription required), external

Liverpool za ta jira har zuwa kasuwar sayar da ‘yan wasa ta watan Janairu don siyan zakakurin dan wasa bayan kokarin da kungiyar ta ke yi domin siyan dan wasan tsakiyar Sfaniya Martin Zubimendi mai shekara 25, daga Real Sociedad ya ci-tura. (Football Insider), external

Fulham ta sake tattaunawa da Manchester United domin sayan dan wasan tsakiyar Scotland Scott McTominay mai shekara 27. (Sky Sports), external

Darektan wasanni na Napoli Giovanni Manna ya ki ya bayanna makomar McTominay. (Manchester Evening News), external

Kungiyar ta Serie A ta amince ta sayi dan wasan gefen Brazil David Neres mai shekara 27 daga Benfica. (Fabrizio Romano), external

Las Palmas ta yi wa Fulham tayin siyan dan wasanta da kuma na Brazil Carlos Vinicius, mai shekara 29 wanda Corinthians ke zawarcinsa. (Sky Sports), external

Crystal Palace ta samu nasara a cinikin da ta ke yi kan dan wasa mai tsaron baya Faransa da Wolfsburg Maxence Lacroix mai shekara 24 (Sky Germany), external