Real Madrid ta fara La Liga da raba maki da Mallorca

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Real Madrid ta fara kare kofin La Liga da tashi 1-1 a gidan Real Mallorca ranar Lahadi a wasan makon farko a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.

Real ta fara cin ƙwalllo ne ta hannun Rodrygo a minti na 14 da take leda, haka suka je hutu, Real tana da ƙwallo ɗaya a raga.

Bayan da suka je hutu suka koma zagaye na biyu ne mai masukin baƙi ta farke ta hannun Vedat Muriqi.

Real ta kare wasan da ƴan ƙwallo 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Ferland Mendy jan kati daf da za a tashi, sakamkon ketar da ya yi wa Vedat Muriqi.

A kakar bara a gasar ta La Liga, Real doke Mallorca 1-0 ta yi gida da waje.

Ranar Asabar, Barcelona ta je ta ci Valencia 2-1 a wasan makon farko a La Liga.

Ranar Laraba Real Madrid mai rike da La Liga na bara ta ɗauki Uefa Super Cup na bana, bayan da ta ci Atalanta 2-0 a Warsaw a Poland.

Real ce ta lashe kofin La Liga a kakar da ta wuce da kuma Champions League.

Za a kammala wasannin makon farko a La Liga ranar Litinin 19 ga watan Agusta, inda za a kara tsakanin Valladolid da Espanyol da na Villarreal da Atl Madrid.

Wasannin mako na biyu

Ranar Juma'a 23 ga watan Agustan 2024

  • Celta Vigo v Valencia
  • Sevilla v Villarreal

Ranar Asabar 24 ga watan Agustan 2024

  • Osasuna v Mallorca
  • Barcelona v Ath Bilbao
  • Getafe v R. Vallecano
  • Espanyol v Sociedad

Ranar Lahadi 25 ga watan Agustan 2024

  • Real Madrid v Valladolid
  • Leganes v Las Palmas
  • Alaves v Real Betis
  • Atl Madrid v Girona

Ƴan ƙwallon da suka buga wa ƙungiyoyin wasan La Liga

Ƴan wasan Mallorca 11: Greif, Maffeo, Raillo, Valjent, Mojica, Samu, Mascarell, Darder, Dani Rodriguez, Asano, Muriqi

Masu jiran ko-ta-kwana: Leo Ramon, Cuellar, Mateu, Lato, Copete, S.V. Heyden, Morlanes, Abdon, Larin, Antonio Sanchez, Domenech, Luna.

Ƴan wasan Real Madrid 11: Courtois, Carvajal, Rudiger, Militao, Mendy, Tchouameni, Valverde, Bellingham, Rodrygo, Vinicius Junior, Mbappe

Masu jiran ko-ta-kwana: Lunin, Fran Gonzalez, Modric, Arda Guler, Endrick, Lucas Vasquez, Vallejo, Ceballos, Fran Garcia, Brahim, Jacobo Ramon.

Wasan farko da Kylian Mbappe ya buga a La Liga, bayan da ya lashe Uefa Super Cup ranar Laraba.