Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Iran ta yi korafi kan cire sunan Allah a tutar kasar da Amurka ta yi
Hukumar kwallon kafa ta Iran ta yi korafi ga Fifa kan cire kalmar sunan Allah a jikin tutar kasar a kafar sada zumunta da tawagar Amurka ta yi.
Kafin kasashen su kara a Gasar Kofin Duniya ranar Talata a cikin rukuni na biyu a Qatar, Amurka ta cire kalmar a sakon da ta saka a kafar sada zumunta a Twitter da Facebook da kuma Instagram.
Amurka ta ce ta cire kalmar ne ''domin nuna goyon baya ga matan Iran da suke neman yanci'', kan zanga-zangar kyamar gwamnatin kasar.
An fara zanga-zangar ne a cikin watan Satumba. bayan da wata matashiya mai shekara 22 ta mutu a hannun 'yan hizbah kan zargin karya dokar rufe gashi.
Kafar yada labaran gwamnatin Iran IRNA ta ce ''A wani abu da ke nuna rashin gogewa a shafin hukumar kwallon kafar Amurka, ta cire sunan Allah a tutar Iran''.
''Hukumar kwallon kafar Iran ta tura sako ga Fifa, domin a ja kunnen Amurka a kuma gargade ta.''
Mai magana da yawun Amurka ya ce an cire sakon sannan an maye gurbin tutar ainahi maras kuskure, sai dai ya kara da cewar ''Muna ci gaba da goyon bayan mata a Iran.''
Iran ta zargi Amurka da kawayenta kan kitsa zanga-zanga, inda gwamnatin Amurka ta kara sa takunkumi kan wasu jami'an gwamnatin kasar.
Amurka da Iran sun katshe huldar diplomasiyya tsakaninsu a 1980.