Shin ko maganin gyaran jiki na Collagen na hana motsewar fata?

Asalin hoton, Getty images
Yaya maganin gyaran fata na Collegen ke taimakawa wajen rage motsewar fata tare da inganta kyawun fata.
Ana dillancin maganin Collegen da ke zuwa a nau'o'i daban-daban da suka haɗar da ƙwaya da gari ko ma alewa a shafukan intanet da shagunan sayar da magunguna da abinci.
Duk da irin shaharar da maganin ya yi, har yanzu babu wata ƙwaƙwarar hujja a kimiyyance da ke tabbatar da sahihanci da ingancinsa: Na ƙara wa fata kyau, tare da rage motsewar fatar da kuma ƙarfinta da ɓoye tabo a jikin fata
Collagen wani muhimmin sinadari ne da ake samu a cikin jikin ɗan'adam, wanda ke da ƙe ƙarfafa da ingancinta da wasu sinadarai da ke aiki cikin tsokar mutane ta yadda za su taimaka wajen inganta kyawun fatar.
Yayin da tsufa ya riski mutum, wannan magani zai rage wa fata irin motsewar da ta yi, tare da kore duk wata yanƙwanewar fata.
"Saboda raguwar samar da maganin, masana'antar ta ba da shawarar ƙara ɓullo da nau'o'in sidanaran da ake amfani da su wajen samar da magungunan, tana mai cewa samun sinadaran zai taimaka wajen haɓaka samar da collagen," in ji Elisete Croco, shugaban sashen nazarin kayayyakin kwalliya na jami'ar Brazil.
To sai dai ana ci gaba da aza ayar tambaya ko maye gurbin sabbin nau'o'in sinadarin na da fa'idodi ko a'a , in ji Croco.
"Amsar na iya kasancewa a cikin isasshen abinci, tare da daidaitaccen sinadarin amino acid ta hanyar abinci. Abin takaici, shaidar kimiyya game da tasirin samfuran ba su da yawa.''
Likitan ya bayyana cewa, wasu binciken sun sami damar nuna cewa, ta hanyar duban dan ta yi, an samu ingantuwar fatar jikin matan da ke amfani da waɗannan kayayyakin.
"Amma yana da mahimmanci a fahimci cewa masana'antar ce ta gudanar da waɗannan binciken ta hanyar nazarin marasa lafiya 20 zuwa 30, wanda kuma ya yi kaɗan a matsayin samfurin bincike."
Nau'ika da matsalolin magungunan Collagen
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Akwai nau'ikan Collagen daban-daban. Daga cikin manyan su akwai:
Verisol - ''Wannan shi ne nau'in maganin da aka fi saya, wanda nau'i ne na collagen 1,'' kamar yadda Mariele Bevilaqua, likitar fata a asibitin Moinhos de Vento, Porto Alegre, da ke Brazil, ta bayyana wa BBC.
Verisol ya ƙunshe da wasu sidanarai da ke taimaka wa wajen rage yanƙwanear fata.
"Amma yana da kyau a lura cewa dukkan nau'ikan sinadarn ana samunsu ne daga jikin wasu nau'ikan dabbobi, kamar fata da ƙasusuwan shanu ko aladu ko kifi ko wasu nau'ikan tsuntsaye''.
Dakta Elisete Croco ya ce maganin ka iya zama mai amfani a wasu lokuta.
"Ina bai wa marasa lafiya shawarar cewa za su iya fara shan maganin aƙalla wata guda kafin fara yi musu aikin fata. Hakan zai sa fatar ta samu sinadaran da take buƙata da za su daidaita sinadanan maganin bayan an yi musu aikn fata a asibiti'', in ji Bevilaqua.
Wata ƙarin matsalar da ake iya samu kan maganin Collegen ita ce matsalar da ta dangancin ƙashi.
"Yana da matuƙar muhimmanci a san cewa babban amfanin da maganin ke yi ba shi ne hana tauyewar fata ba, sai dai kare ta daga yanƙwanewar,'' in ji Croco.
"Fara amfani da maganin tun a lokacin shekarun ƙuriciya, tare da cin abinci mai gina jiki a lokacin da mutum ya kai shekara 50 na da matuƙar muhimmanci."
Dakta Mariele Bevilaqua ta bayyana wasu matakan da ya kamata a bi domin kare fata daga lalacewa, kamar fita rana, da kauce wa shaye-shaye, da cin abinci mai kyau, da yawan shan ruwa da samun wadataccen barci.
Ta ƙara da cewa idan mutum ya gano wasu matsaloli a fatarsa, kamar ƙuraje ko yanƙwanewar fara da wasu taɓo a fatar, maganin na ɗauke da sinadararn da ke magance waɗannan matsaloli, to amma ta ce yana da kyau a riƙa auna mutane saboda kowa na da tasa matsalar.
"Wata hanyar ita ce mayar da hankali maganguna waɗanda ba allurai ba, yin amfani da hanyoyin gargajiya wajen magance matsalolin'', in ji Croco.
"Za ka iya amfani da wasu hanyoyin kamar cire ƙuraje ta hanyar matsasu don fitar da ruwansu, musamman idan ka fara manyanta'', in ji likitar.












