Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa ƴan Najeriya ke zanga-zanga?
- Marubuci, Nkechi Ogbonna
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Lagos
- An wallafa
Kayan abinci na yau da kullum sun yi wa yawancin 'yan Najeriya tsada
Yayin da wasu ke bayyana ɓacin ransu a shafukan Intanet, a wasu sassan Najeriya, jama'a na fitowa kan tituna domin nuna rashin jin daɗinsu kan hauhawar farashin kayan abinci da ake ci gaba da fama da ita a ƙasar, wadda ita ce ta ta fi kowace ƙarfin tattalin arziki a Afirka.
A duk faɗin duniya, tsadar rayuwa na yin matuƙar tasiri kan mutane.
Sai dai a Najeriya, abin ya ƙara taɓarɓarewa sakamakon cire tallafin man fetur da gwamnati ta yi da kuma yadda darajar kuɗin ƙasar ke ci gaba da faɗuwa, kan kudaden kasashen waje.
Me ke ɓata wa ƴan Najeriya rai?
Yunwa ce babban dalilin ɓacin ran mutane da ya sa ƴan Najeriya suka fito zanga-zanga. A baya-bayan nan dai dubban mutane ne suka fantsama kan tituna a jihohin Neja da Kogi da ke arewacin ƙasar inda suka buƙaci a ɗauki matakin gaggawa wanda zai magance tsadar rayuwa.
A jihar Kano wasu mazauna jihar sun nuna ɓacin ransu kan tsadar kayan abinci da suka haɗa da shinkafa da gero da masara. Jihar na da mutane miliyan 10 da ke fama da talauci, wanda shi ne mafi yawa a ƙasar.
A ranar Juma’ar da ta gabata ne ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya NLC ta bai wa gwamnatin ƙasar wa’adin kwanaki 14 don warware matsalar tattalin arziƙi, inda ta yi barazanar gudanar da zanga-zanga a ranakun 27 da 28 ga watan Fabrairu.
Ƙungiyar ta ce lamarin ya fi ƙamari tsakanin ma’aikatan gwamnatin Najeriya da ke karɓar mafi ƙarancin albashi na Naira 30,000 ($20) a wata.
Bankin raya ƙasashen Afirka (AfDB) ya yi gargadin cewa Najeriya tare da Habasha da Angola da kuma Kenya na fuskantar haɗarin samun tashe-tashen hankula a tsakanin al’umma sakamakon hauhawar farashin man fetur da na kayan masarufi.
Wane irin tsada abinci ya yi a Najeriya?
A makon da ya gabata, Hukumar Kididdiga ta Najeriya (NBS) ta ce hauhawar farashin kayayyaki ta kai kashi 29.9%, mafi girma a cikin kusan shekaru 30 da suka gabata, sakamakon tsadar kayan abinci da ya kai kashi 35.4%.
Burodi wanda shi ne abincin karin kumallo a gidaje da dama a faɗin ƙasar, ya tashi daga Naira 500 ($0.33) zuwa sama da 1,500 ($0.87) a cikin shekara guda.
Sauran kayan abinci irin su ƙwai da kifi da nama da shinkafa, sun sami matuƙar tashin farashi.
Buhun shinkafa mai nauyin kilogiram 50, wanda shi ne abinci mafi farin jini a gidaje da dama, ya tashi daga Naira 35,000 zuwa Naira 75,000 a cikin shekara guda.
Wane abinci mutane ke ci yanzu?
A yankin arewacin ƙasar, mazauna yankin sun fara tattara dusar shinkafa suna amfani da ita a matsayin abinci.
Akan yi amfani da dusar ne wurin haɗa abincin kifi, amma wasu mutane yanzu suna amfani da ita a matsayin abincinsu.
Hotunan bidiyo na shafukan sada zumunta sun kuma nuna gidajen Najeriya da dama sun rage hannu a yawan abincin da suke ci a gida.
Wani bidiyo ya nuna yadda wata mata ke yanka kifi ɗaya kashi tara maimakon kashi huɗu zuwa biyar. Tana cewa burinta shi ne tabbatar da cewa iyalinta sun iya cin kifi sau biyu a rana.
Mene ne gwamnati ke yi?
Mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima ya sanar da shirin gwamnati na kafa hukumar da za ta kula da farashin kayan abinci a ƙasar.
Gwamnatin ta kuma umarci a buɗe rumbunan hatsin gwamnatin tarayya, a kuma raba wa al’umma tan 42,000 na hatsi da suka haɗa da masara, da gero.
Wannan dai ba shi ne karon farko da gwamnati ta ce tana rabon tallafin ga talakawa da marasa galihu a Najeriya ba, sai dai ƙungiyoyin ƙwadago sun sha sukar tsarin raba abinci da gwamnati ke yi, suna cewa yawancin abin ba ya kai wa ga iyalai marasa galihu.