Bellingham ya ci kwallo na 12 a La Liga a gidan Betis

Jude Bellingham

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Real Betis da Real Madrid sun tashi 1-1 a wasan mako na 16 a gasar La Liga da suka kara ranar Asabar a Villamarin.

Real ce ta fara cin kwallo ta hannun Jude Bellingham bayan da suka koma zagaye na biyu, sai Betis ta farke ta hannun Aitor Ruibal.

Kawo yanzu Bellingham dan wasan tawagar Ingila ya ci kwallo 12 a La Liga, wanda ya koma Real Madrid kan fara kakar bana daga Borussia Dortmund.

Da wannan sakamakon Real Madrid ta yi wasa 14 a jere ba tare da an doke ta ba a dukkan fafatawa da canjaras uku daga ciki.

Rabonda Real Madrid ta yi rashin nasara a La Liga tun 3-1 da aka doke ta a Atletico Madrid ranar 24 ga watan Satumbar 2023.

Real Madrid tana matakin farko a teburin La Liga da maki 39, bayan wasa 16, sai a ranar Lahadi Girona wadda take ta biyu mai maki 38 za ta je Barcelona ta uku mai maki 34.

Ranar Talata 12 ga watan Disamba, Real Madrid za ta je Union Berlin domin buga wasan karshe a cikin rukuni na uku a Champions League.

Daga nan Real za ta karbi bakuncin Villareal ranar 17 ga watan Disamba, sannan ta je Alaves ranar 21 ga watan Disamba.

Daga nan za a yi hutun Kirsimeti a gasar La Liga, sai kuma cikin Janairun 2024 a koma fafatawar.

Wasannin da za buga ranar Lahadi:

  • Atletico Madrid da Almeria
  • Granada da Athletic Bilbao
  • Cadiz da Osasuna
  • FC Barcelona da Girona