Man City da Chelsea na rububin Simons, Roma na zawarcin Bailey

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Watakila Manchester City ta sha gaban Chelsea a zawarcin da ta ke yi wa dan wasan RB Leipzig dan kasar Netherlands, Xavi Simons, mai shekara 22. (Talksport)

Brighton za ta bukaci sama da fam miliyan 100 kan Carlos Baleba bayan Manchester United ta nuna sha'awar daukar dan wasan tsakiyar Kamaru mai shekaru 21 . (Telegraph - subscription required)

Dan wasan gaban Denmark Rasmus Hojlund na son ya bar Manchester United a wannan bazarar yayin da AC Milan ke kokarin tattaunawa kan yarjejeniyar aro tare da zabin sayar da shi.(Gazzetta dello Sport - in Italian)

Manchester City ta saka Magnes Akliouche na Monaco cikin jerin 'yan wasan da take zawarci, kuma za ta yi gogayya da Bayer Leverkusen kan sayen dan wasan gefe na kasar Faransa mai shekara 23.(Florian Plettenberg)

Roma na tattaunawa da Aston Villa kan batun daukar Leon Bailey amma har yanzu a hukumance ba ta kaiga yanke shawarar siyan dan wasan gefe na Jamaica mai shekaru 28, wanda kuma ke jan hankalin kungiyoyin Besiktas da Saudi Pro League. (Athletic - subscription required)

Fulham na son ta kafa sabon tarihi a cinikin 'yan wasa inda ta ke son ta zarce fan miliyan 34 don siyan dan wasan gefe na Shakhtar Donetsk dan kasar Brazil Kevin, mai shekara 22.(Sky Sports)

Southhampton a karo na biyu a jere ta sake yin gyara kan tayin da Everton ta yi mata kan Tyler Dibling bayan ta ki amincewa da tayi sau uku da Toffees suka yi kan dan wasan gefe na Ingila mai shekara 19. (Florian Plettenberg)

Manchester United na ganin Chelsea na son daukar Alejandro Garnacho, amma Blues na fatan samun dan wasan na Argentina mai shekara 21 a kan kudi kasa da farashin da United ta nema na fan miliyan 50. (Sky Sports)

Nice na ci gaba da tattaunawa da Crystal Palace kan cinikin dan wasan gaban Faransa Odsonne Edouard mai shekaru 27.(Footmercato - in French)

Bayern Munich ta yi tayin fan miliyan 52, da kari da kuma kaso kan duk wani cikinikin sake sayar da dan wasan gaban Jamus, Nick Woltemade, amma Stuttgart na bukatar fan miliyan 65.(Sky Sports Germany)