Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ya dace da rafli Kavanagh ya bai wa Rice jan kati a wasan Brighton
Alkalin wasa, Chris Kavanagh ya yi hukuncin da ya dace na bai wa Declan Rice jan kati a Premier League a karawa da Brighton, in ji wani kwamiti mai zaman kansa.
Kwamitin da yake bitar yadda aka busa wasannin babbar gasar tamaula ta Ingila a duk mako, ya ce ya dace da aka kori Rice daga karawar.
Tun farko an bai wa Rice katin gargadi, sai ya taɓa ƙwallo a lokacin da Joel Veltman zai yi bugun tazara a minti na 49.
Lamarin ya faru ne a wasan Premier League mako na uku da suka tashi 1-1 tsakanin Arsenal da Brighton a Emirates ranar Asabar 31 ga watan Agusta.
Shi ne jan katin farko da aka yi Rice a tarihin tamaularsa, inda kwamitin ya ce yana sane ya taɓa ƙwallon, kenan hukuncin ya dace da shi, wanda tun farko yana da kati mai ruwan ɗorawa.
Lokacin da lamarin ya faru Gunners ta ci ƙwallo ta hannun Kai Havert, daga baya Joao Pedro ya farke da ta kai Brighton ta samu maki ɗaya a Emirates.
Kwamitin mai zaman kansa ya ƙunshi tsoffi uku ko dai ƴan wasa ko masu horar da tamaula da wakili daga Premier League da wani daga raflin gasar.
Haka kuma kwamitin ya ce VAR ta yi daidai da hukuncin da ta yanke a ƙwallon da Trent Alexander-Arnold ya ci a wasan da Liverpool ta ci Manchester United 3-0 a Old Trafford.
Tun farko an karɓi ƙwallon da Arnold ya ci daga baya aka soke da cewar Mohamed Salah ya yi satar aiki.
Cikin hukuncin da kwamitin ya yanke ya ce sau ɗaya ne aka samu kuskure daga abu 23 da suka yi bita a wasannin Premier League mako na uku.