Na fi kowa dace da zuwana United -Casemiro

An wallafa

Sabon dan wasan da Manchester United ta dauka Casemiro ya ce ya fi "kowanne dan wasa farin ciki" bayan komawarsa kungiyar, ta yadda zai rika buga wasa da dan kasarsa Fred.

Dan wasan tsakiyar ya koma United ne daga Real Madrid a wannan makon kan kudi fan miliyan 70.

An gabatar da dan Brazil din mai shekara 30 a Old Trafford ne gabanin fara wasan kungiyar da Liverpool, wanda United ta yi nasara da ci 2-1 a ranar Litinin.

Ta samu nasarar be bayan kashin da ta sha sau biyu a gasar Premier a wannan kakar, kuma Fred na cikin wadanda magoya baya ke suka.

Casemiro ya bayyana cewa ya tattauna da Fred kafin ya koma United.

"Abokin ne wanda muka yi wasa da yawa da shi a Brazil shekaru masu yawa."

Ya kara da cewa: "Babban dan kwallo ne shi yasa ma yake taka leda a United da Brazil Fred yana da gogewa sosai.

"Dan wasa ne da ke iya karade ko ina a cikin fili, yana iya bayar da kwallo yadda ya kamata da kowacce kafa".

Casemiro ya kuma sake haduwa da Cristiano Ronaldo da Raphael Varane a Man United, bayan taka ledar da suka yi su ukun a Real Madrid.