Me kuke son sani kan wasan Portugal da Jamhuriyar Czech?

Euro 2024

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Portugal da Jamhuriya Czech za su kara ranar Laraba a wasan farko a rukuni na shida a gasar cin kofin nahiyar Turai a Jamus, Euro 2024.

Tawagogin sun saba haduwa a Euro a tsakaninsu, wannan shi ne wasa na hudu da za su kece raini a gasar.

Czech ce ta yi nasara 1-0 a Euro 1996, sai Portugal ta ci Czech 3-1 a Euro 2008 da kuma 1-0 a Euro 2012.

A kuma lokacin da suka fafata Cristiano Ronaldo ya ci Jamhuriyar Czech kwallo a Euro 2008 da kuma a Euro 2012.

Ita kanta Czech tana da mai ci mata kwallaye Ivan Hašek, wanda ya zura biyar a raga, iri daya da yawan na Ronaldo a Euro 2020.

Portugal ta yi nasarar doke Czech a wasa hudu baya har da uku da kwallo bai shiga ragarta ba.

Dukkansu sun kai quarter finals a Euro 2021, inda Portugal ta yi rashin. nasara a hannun Belgium, ita kuwa Denmark ta fitar da Czech.

Yayin da Portugal ta dauki Euro 2016, haka itama Jamhuriyar Czech ta lashe a Euro 1976 a lokacin da take tare da Czechoslovakia.

Kociya, Roberto Martínez shi ne ya ja ragamar tawagar da ta yi waje da Portugal a kakar a Euro 2020 da aka gudanar da wasan karshe a Wembley.

Yanzu kuma shi ne ke horar da Portugal, wadda ta samu gurbin Euro 2024 ba tare da rashin nasara ba.

Portugal ta ci kwallo 36 aka zura mata biyu a raga, wadda ta samu gurbin shiga wasanni Jamus tun kan saura wasa uku a karkare karawar neman shiga gasar.

Cristiano Ronaldo zai zama na farko da zai buga Euro karo na shida, mai kwallo 14 a raga jimilla a wasannin.