Manchester United ta kammala ɗaukar Leny Yoro daga Lille

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Manchester United ta ɗaukar ɗan bayan Faransa Leny Yoro daga Lille kan kwantaragin shekara biyar kan kuɗi fan miliyan 52.1.

Ɗan wasan bayan zai zauna a Old Trafford har zuwa 2029, da kuma zaɓin karin watanni 12 idan kwantaragin ta ƙare.

Yoro wanda ya fara bugawa Lille lokacin yana da shekara 16, kuma Real Madrid da Paris St-Germain duka sun neme shi, a gefe guda kuma Liverpool ta nuna sha'awarta kan ɗan wasan.

Ya buga wasanni 32 a kakar da ta kare ta bara ya kuma ci kwallo biyu yayin da ya taimaka wa Lille suka gama gasar a mataki na hudu kuma sunan sunansa ya fito cikin tawgar gasar ta bara.

"Bugawa babbar ƙungiyar kwallon kafa mai buri irin Manchester United a farkon shekaruna na kwallo ba ƙaramin abin girmamawa ba ne a wurina," in ji Yoro.

"Tun farkon tattaunawarmu da ƙungiyar suka shirya yadda za su taimakan na habbaka a wannan kungiyar, sun kuma nuna damuwa kaina da iyalaina.

"Na san matasan 'yan wasa da dama matasa da suka taso a Man United, kuma a gani nan ne wurin da zan iya habbaka kwallona, tare da sabbin abokan kwallona. Na ƙagu na fara buga kwallo a kungiyar."