Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man United ta kammala cinikin Hojlund
Manchester United ta kammala sayen dan wasan gaban Denmark Rasmus Hojlund daga Atalanta kan fam miliyan 72.
Dan wasan mai shekaru 20, wanda ya koma kungiyar ta Serie A a shekarar 2022 kuma ya ci kwallaye 10 a wasanni 34 da ya buga a bara, ya koma Old Trafford kan kwantiragin shekaru biyar.
Shi ne dan wasa na uku da kocin United Erik ten Hag ya dauko a bazaran nan bayan ya dauko Mason Mount daga Chelsea kan fam miliyan 55, sai kuma golan Inter Milan Andre Onana ya zo kan fam miliyan 47.2.
Rahotanni sun ce zakarun Ligue 1 Paris St-Germain sun yi zawarcin Hojlund a matsayin wanda zai maye gurbin Kylian Mbappe, wanda ba a tabbatar da makomarsa ba.
Hojlund ya fara wasa a Copenhagen, inda ya fara wasan Danish Superliga yana da shekara 17 a cikin 2020 kafin ya koma kungiyar Sturm Graz ta Austria bayan shekaru biyu.
Watanni shida kacal ya yi a gasar Bundesliga ta Austria bayan ya koma Sturm a watan Janairun 2022 amma ya zura kwallo tara a raga a wasanni 17 da ya buga.