Lukaku zai bar Chelsea, Juve na duba batun Sancho, Arsenal na neman dan wasa

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Chelsea na son mai kai hari na Ingila mai taka leda a Everton, wato Dominic Calvert-Lewin, dan shekara 27, a matsayin zabi mai rahusa idan aka kwatanta da dan wasan Najeriya mai taka leda a Napoli Victor Osimhen, mai shekara 25, wanda ya yi dan karen tsada. (Sun)

Juventus ta bukaci Manchester United ta biya wani kaso na kudin dan wasa Jadon Sanchodomin maida dan wasan na Ingila mai shekara 24 kungiyar. (Gazzetta dello Sport - in Italian)

Arsenal na neman sayo karin dan wasa mai kai hari, da zarar sun kammala dauko dan wasan tsakiya na Sifaniya Mikel Merino, 28, daga Real Sociedad. (Mirror)

Da alama tayin aron dan wasa Armando Broja daga Chelsea na gab da durkushewa, bayan sakamakon binciken likita na dan wasan mai shekara 22, da ke kai hari a kungiyarsa ta Albania ya nuna ya ji rauni (Sun)

Mai kai hari na Belgium Romelu Lukaku, 31, zai bar kungiyar Chelsea dmin komawa Napoli kan kwantiragin shekara 3. (Mirror)

Leicester City na tattaunawa domin dauko mai kai hari na tsakiya dan Morocco Bilal El Khannouss, inda kungiyarsa ke neman fam miliyan 17 kafin saida dan wasan mai shekara 20. (HITC)

Wolves na tattauna dauko matashin dan wasan Burnley mai shekara 19, a ajin 'yan shekara 21 wato Luca Koleosho. (Express & Star)

Dan wasan tsakiya na Chelsea Tino Anjorin, mai shekara 22, ya amince ya koma Empoli a Serie A, inda tsohon dan wasan na Ingila ya amince ya koma bisa radin kai ba tare da ko kwabo ba. (Fabrizio Romano)

Golan Brazil Alisson, mai shekara 31, na tattaunawa da kungiyar Liverpool, bayan ya yi watsi da tayin da kuluf din Saudiyya ya yi masa, sai dai kuma Reds na hakilon golan Valencia Giorgi Mamardashvili, mai shekara 23. (Telegraph - subscription required)