Arsenal ta ci wasa na biyu a jere ƙwallo bai shiga ragarta ba a Premier

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Arsenal ta je ta doke Aston Villa 2-0 a wasan mako na biyu a Premier League da suka kara a Villa Park ranar Asabar.

Ƙungiyoyin biyu sun je hutu ba ci a tsakaninsu, inda sai da suka koma zagaye na biyu ne Arsenal ta zura ƙwallo biyu a ragar Aston Villa.

Leandro Trossard ne ya fara cin ƙwallo, sannan Thomas Partey ya kara na biyu a raga a wasan na hamayya.

Da wannan sakamakon Gunners ta hada maki shida da cin ƙwallo huɗu, ba tare da an zura mata ko ɗaya ba kawo yanzu da fara wasannin bana.

Wannan nasarar ga Arsenal gagarumar ci gaba ce a shirin da take na lashe Premier League na bana, bayan da Villa ta doke ta gida da waje a bara.

Villa ta ci Arsenal 1-0 a Premier League a Villa Park ranar 9 ga watan Disambar 2023, sannan ta je Emirates ta zura 2-0 a ranar 14 ga watan Afirilun 2024.

Ranar Asabar 17 ga watan Agusta, Gunners ta doke Wolves 2-0 a wasan makon farko a babbar gasar tamaula ta Ingila.

Gunners ɗin za ta karɓi bakuncin Brighton a wasan mako na uku ranar Asabar 31 ga watan Agusta a Emirates.

Brighton ta fara kakar bana da kafar dama, bayan da ta je ta doke Everton 3-0 a Goodison Park, sannan ta yi nasara a kan Manchester United 2-1 ranar Asabar.