Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan ne karo na uku da Barca ta fara La Liga da tagomashi
Barcelona tana matakin farko a kan teburin La Liga da maki 18, sakamakon lashe wasa shida a jere da fara kakar nan.
Ranar Lahadi, Barcelona karkashin Hansi Flick ta je ta doke Villareal 5-1 a karawar mako na shida a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.
Kawo yanzu Barcelona ta zura ƙwallo 22 a raga daga wasa shida, inda biyar ne suka shiga ragarta a La Liga.
Wannan shi ne karo na uku da Barcelona kan fara La Liga da kafar dama, guda biyun ta yi karawa sama da shida ba tare da rashin nasara ba.
Kuma karo na bakwai da Barcelona kan sa ƙwazo da fara kaka a dukkan fafatawa, sai dai biyu daga ciki ta haura yawan karawa shida tana yin nasara.
Mai horarwa Tata Martino, shi ne ya yi nasarar cin karawa takwas a 2013/14, sai kuma koci, Ernesto Valverde, wanda ya yi nasara bakwai a jere a 2017/18.
Sai kuma Hansi Flick da ya ci shida daga wasa shida da fara La Liga ta kakar nan.
Ranar Laraba, Barcelona za ta karɓi bakuncin Getafe a wasan mako na bakwai a La Liga, inda Flick ke fatan ci gaba da kafa tarihi a gasar ta La Liga.
Sauran kociyan da suka ja ragamar Barcelona da lashe wasa shida da fara kaka sun haɗa da James Bellamy a 1929/30, sai kuma Johan Cruff a 1990/91.
Haka shima Louis van Gaal ya yi wannan bajintar a 1997/98 da Pep Guardiola a 2009/10 da kuma Tito Vilanova a 2012/13/