Jota zai yi jinyar wata ɗaya in ji Klopp

Diago Jota

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Kociyan Liverpool, Jurgen Klopp ya ce Diogo Jota zai yi jinyar wata ɗaya, bayan raunin da ya ji a gwiwa a karawa da Brentford ranar Asabar.

An sauya Jota a wasan tun kan hutu, bayan da ɗan kwallon Brentford, Christian Norgaard ya faɗo masa a kan kafa.

Kenan Jota ba zai buga wa Liverpool wasan mako na 26 da za ta kara da Luton ba ranar Laraba, bayan da wasu rahotanni ke cewar zai yi jinyar wata biyu.

Amma dai ana sa ran zai koma taka leda kan kammala kakar bana, domin ya samu damar buga wa Portugal gasar kofin nahiyar Turai Euro 2024.

Jota, wanda ya ci kwallo 14 a wasa 28, shi ne gwarzon ɗan wasan Liverpool a watan Janairu, sai dai ba zai buga wasan karshe a Carabao Cup da Chelsea ranar Lahadi ba.

Haka shi ma ɗan wasan Liverpool, Curtis Jones ya ji rauni a karawa da Brentford, an kuma sauya Darwin Nunuz a fafatawar.

Mai tsaron raga, Allison Becker bai samu buga wasan ba, bayan rauni da ya ji a lokacin atisaye tun kan ranar fuskantar Brentford.

Ƴan wasan Liverpool da ke jinya sun haɗa da Trent Alexander-Arnold da Dominik Szoboszlai da kuma Thiago Alcantara.