Za a gurfanar da ɗan uwan Rashford a kotu

Asalin hoton, MIAMI DADE COUNTY
Ɗan uwa kuma wakilin tauraron Manchester United Marcus Rashford zai gurfana a gaban wata kotu a Amurka bayan kama shi da laifin cin zarafi.
Rahoton 'yan sanda ya ce Dane Rashford, mai shekara 31, yana tafiya ne a bayan wata Uber tare da wata mata bayan ya ziyarci wani gidan rawa na Miami a ranar 20 ga watan Oktoba.
Matar da ke zargin ta yi iƙirarin cewa an yi mata naushi sau biyu a fuska.
A cikin rahoton 'yan sanda, wanda BBC ta gani, wani jami'i ya bayyana yin hulɗa da wanda abin ya shafa da sanyin safiya bayan an kira shi zuwa wani otal da ke Miami Beach.
Jami’an sun ɗauki bayanan matar da abin ya shafa, da Mista Rashford da ‘yar uwarsa, Chantelle Maynard, kafin suka kama Mista Rashford suka kuma tuhume shi da laifi cin zarafi.
An shirya sauraron karar ranar 27 ga watan Nuwamba.








