Liverpool ta shiga jerin wadanda suka ci tara a Premier League

Liverpool

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Ranar Asabar Liverpool ta hada maki uku a karon farko a gasar Premier League ta bana, bayan da ta casa Bournemouth 9-0 a wasan mako na hudu a Anfield.

Roberto Firmino ya ci biyu da shi da Luis Diaz, sai Harvey Elliott, wanda ya ci kwallon farko a Premier League da kuma Fabio Carvalho.

Sauran da suka ci kwallayen sun hada da Trent Alexander-Arnold da Virgil van Dijk da kuma Chris Mepham, wanda ya ci gida.

Ga jerin kungiyoyin da suka ci kwallo tara a gasar Premier League

Manchester United 9-0 Southampton, Fabrairun 2021

An fara bai wa Alexandre Jankewitz jan kati kafin minti daya da take leda a wasansa na farko a matakin kwararren dan kwallo, tun daga nan Southampton ta rasa ta kanta.

Anthony Martial ya zura biyu a raga, sai dan kwallon Southampton Roman Bednarek ya ci gida, aka bashi jan kati.

Sauran da suka ci wa United kwallayen sun hada da Aaron Wan-Bissaka da Marcus Rashford da Edinson Cavani da Scott McTominay da Bruno Fernandes da kuma Daniel James.

Southampton 0-9 Leicester, Oktoban 2019

An bai wa dan kwallon Southampton jan kati, wato Ryan Bertrand, bayan da ya yi wa Ayoze Perez keta a lokacin da za a ci kwallo.

Ben Chilwell ne ya fara cin kwallo a minti na 10 da fara tamaula, sai Perez da ya zura uku rigis a raga.

Shima Jamie Vardy ya ci uku rigis a wasan – ta ukun a bugun fenariti, sai Youri Tielemans da kuma James Maddison kowannensu ya ci kwallo.

Tottenham 9-1 Wigan, Nuwambar 2009

Dan kwallon Tottenham, Jermain Defoe ya zura biyar a raga, sauran da suka ci kwallaye sun hada Aaron Lennon da Peter Crouch da David Bentley da kuma Niko Kranjcar.

Wigan ta zare daya ta hannun Paul Scharner.

Manchester United 9-0 Ipswich, Maris din 1995

Andy Cole ne ya ja ragamar United da zura kwallo biyar a raga, sai Mark Hughes da ya ci biyu, sai Paul Ince da Roy Keane da kowanne ya ci kwallo.

A kakar ce Ipswich ta kare a karshen tuburi bayan da aka kammala kakar wasannin.