Trossard aka zaba gwarzon watan Maris a Arsenal

An wallafa

Magoya bayan Arsenal sun zabi Leandro Trossard a matsayin gwarzon dan wasa a watan Maris a kungiyar.

Dan kwallon tawagar Belgium, wanda ya yi wata biyu a Gunners ya samu kuri'a kaso 39 cikin 100, sai Bukayo Saka na biyu, Gabriel Martinelli ne na uku.

A wasa biyar da Trossard ya buga a watan Maris ya bayar da kwallo biyar aka zura a raga, wanda ya koma Gunners a watan Janairu daga Brighton.

Uku daga ciki ya bayar an ci Fulham tun kan hutu a Premier League ya kuma bayar da daya a fafatawa da Everton da kuma a wasan hamayya da Crystal Palace.

Trossard shine na shida da aka zaba gwarzon dan kwallon Arsenal a kungiyar a kakar nan.

Gabriel Jesus ne ya lashe na Agusta, sai Granit Xhaka a Satumba da Oktoba, Ben White a Nuwamba da Bukayo Saka suka a Disamba.

Sai Oleksandr Zinchenko da ya karbi na na Janairu da na Fabrairu.

Ranar Lahadi Arsenal za ta fafata da Liverpool a wasan mako na 30 a gasar Premier League.

Arsenal tana mataki na daya a kan teburin kakar bana da tazarar maki takwas tsakaninta da Manchester City ta biyu.

Liverpool kuwa wadda za ta kare kakar bana ba tare da daukar kofi ba, tana ta takwas a teburin Premier da maki 43.