Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Madrid da za ta karɓi baƙuncin Celta a La Liga
Real Madrid za ta karbi bakuncin Celta Vigo a gasar La Liga karawar mako na 28 da za su kece raini ranar Lahadi a Santiago Bernabeu.
Kungiyoyin sun kara a bana ranar Juma'a 25 ga watan Agustan 2023, inda Real ta yi nasarar cin 1-0.
Kuma Jude Bellingham ne ya ci mata kwallon saura minti tara a tashi daga wasan, sai dai dan kwallon tawagar Ingila ba zai buga karawar ta ranar Lahadi ba.
Kawo yanzu Real ce ta daya a kan teburin La Liga da maki 66 da tazarar maki hudu tsakanin ta da Girona ta biyu, wadda ta yi fafatawa 28.
Barcelona mai rike da kofin bara ce ta uku da maki 61, bayan da ta buga wasa 28, wadda ta ci Real Mallorca 1-0 ranar Juma'a 8 ga watan Maris.
Ita kuwa Celta mai maki 24 bayan wasa 27 a babbar gasar tamaula ta Sifaniya tana ta 17 a kasan teburin bana.
'Yan wasan Real Madrid:
Masu tsaron raga: Lunin, Kepa da kuma Diego.
Masu tsaron baya: Carvajal, Nacho, Lucas Vázquez, Fran García, Rudiger da kuma Mendy.
Masu buga tsakiya: Kroos, Modrić, Camavinga, Valverde, Tchouameni, Ceballos da kuma Arda Guler.
Masu cin kwallaye: Vini Jr., Rodrygo, Joselu da kuma Brahim.
Wasannin da za a buga ranar Lahadi:
- Deportivo Alaves da Rayo Vallecano
- Las Palmas da Athletic de Bilbao
- Real Madrid da Celta Vigo
- Real Betis da Villarreal
- UD Almeria da Sevilla