Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
De Bruyne zai yi jinyar wata hudu
An yi wa dan wasan tsakiya na Manchester City Kevin de Bruyne tiyata saboda raunin da ya ji a kafarsa wanda hakan ka iya hana shi taka leda na tsawon wata hudu.
Dan wasan na Belgium, mai shekara 32, ya ji rauni minti 23 da fara wasan da City ta doke Burnley da ci 3-0 a gasar Premier ranar 11 ga watan Agusta.
A wasan ƙarshe na kofin Zakarun Turai na Champion League ma sai da ɗan wasan ya ji raunin da ya tilasta sauya shi a wasan.
Rahotanni sun bayyana cewa an gudanar da tiyatar ba tare da wata matsala ba kuma dan wasan ya shirya fara murmurewa.
Yanzu City na yunkurin dauko dan wasan da zai maye gurbinsa inda su ke tattaunawa da West Ham kan dan wasan tsakiya Lucas Paqueta, wanda ƙungiyar ta sanya wa farashin fam miliyan 80.