An soke jan katin da aka bai wa Alexis Mac Allister

Alexis Mac Allister

Asalin hoton, BBC Sport

An wallafa

An soke jan kati da aka bai wa Alexis Mac Allister na Liverpool a karawar da suka doke Bournemouth da ci 3-1 a ranar Asabar bayan kungiyar ta daukaka kara.

An kori dan wasan tsakiyan na Argentina, mai shekara 24, kuma an dakatar da shi wasanni uku bayan ya kwashe kafar Ryan Christie a minti na 58 na wasan da aka buga a filin Anfield.

Kocin Liverpool, Jurgen Klopp ya ce matakin ya yi tsauri.

Kungiyar ta Reds ta daukaka kara kuma hukumar kula da harkokin kwallon kafa ta janye jan katin ta kuma dage dakatarwar.