Ko zuwan Mbappe Real Madrid za take amfani da Modric kuwa?

Luca Modric

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Real Madrid ta gabatar da sabon ɗan wasan da ta ɗauka Kyalian Mbappe ranar Talata a gaban magoya baya 80,000 a Santiago Bernabeu.

Kyaftin din tawagar Faransa ya saka hannu kan ƙunshin yarjejeniya a watan Yuli ta kaka biyar, bayan da ƙwantiraginsa ya kare a Paris St Germain a watan Yuni.

To sai dai zuwan ɗan wasan Real Madrid zai kara sa matsi wajen amfani da ƴan wasa 11 da za suke fara buga wa ƙungiyar tamaula a kakar da za a fara ta 2024/25.

Wanda ake tunani daga cikin waɗanda za suke zaman benci har da Luca Modric, ƙyaftin din tawagar Crotia.

Mai shekara 38 ya ci ƙwallo biyu a wasa 46 a kakar da ta wuce a ƙungiyar Sifaniya, wadda Real Madrid ta lashe La Liga da kuma Champions League.

Real Madrid za take amfani da Mbappe a dukkan wasanninta, musamman da Toni Kross ya yi ritaya, ta kuma ɗauki matashi daga Brazil, Endrick.

Haka kuma ɗan wasan Turkiya, Arda Guler na fatan samun damar buga wasa da yawa, wanda ya taka rawar gani a Euro 2024.

Daga yadda tsarin yake kenan Carlo Ancelotti zai ke wasa da Vinicius Jr da Rodrygo da Jude Bellingham da kuma Mbappe.

Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images

Modric zai cika shekara 39 da haihuwa cikin watan Satumba, wasu na cewa ɗan wasan zai wakilci Crotia a gasar kofin duniya a 2026 daga nan ya yi ritaya.

Ba koda yaushe za ka ga ɗan wasa da yawan shekaru yana taka leda ba, amma ya ci ƙwallo a Euro 2024, ya zama mai shekaru da yawa da ya zura ƙwallo a raga a gasar.

Sai dai kuma a gabaki ɗayan wasannin Euro 2024 ɗan wasan Portugal, Pepe shi ne mai yawan shekara da ya buga gasar mai shekara 41 da haihuwa.

Sifaniya ce ta lashe Euro 2024 karo na hudu jimilla, bayan da ta yi nasara a kan Ingila 2-1 ranar Lahadi a birnin Berlin a Jamus.

Luca Modric

Asalin hoton, Getty Images

Luca Modric ya je Real Madrid a 2012, kuma a kaka 12 da ya buga ya zama zakakurin ɗan wasan ƙungiyar kuma fitatce a duniya.

Modric ya lashe kofi 26 a Real Madrid

  • Champions League (6)
  • Club World Cup (5)
  • European Super Cup (4)
  • La Liga (4)
  • Copa del Rey (2)
  • Spanish Super Cups (5)

Ɗan kasar Croatian yana ɗaya daga ƴan wasa biyar a Real Madrid da suka ɗauki Champions League shida, kuma da yawan ɗaukar kofuna a tarihi.

Modric, mai shekara 38, ya saka hannu kan yarjejeniyar kaka ɗaya, domin ci gaba da taka leda a Real Madrid zuwa 30 ga watan Yunin 2025.