Liverpool ta huce a kan Bournemouth a gasar Premier

An wallafa

Liverpool ta ci Bournemouth 9-0 a wasan mako na hudu a gasar Premier League da suka kara a Anfield ranar Asabar.

Karon farko da Liverpool ta zazzaga kwallo tara a raga a wasa a Premier tun bayan da ta taba cin Crystal Palace 9-0 a 1989.

Haka kuma a karon farko da Jurgen Klopp ya ci kwallo tara a wasa a tarihin sana'arsa ta horar da tamaula.

Minti uku da fara wasa Liverpool ta fara zura kwallo ta hannun Luis Diaz daga baya Harvey Elliott ya kara na biyu a minti uku tsakani.

Karon farko da Liverpool ta ci kwallo biyu a raga cikin minti shida a Premier League tun bayan Maris din 1996 da ta yi wa Aston Villa haka.

Boberto Firminho ne ya bayar da dukkan kwallayen biyu aka zura a raga cikin minti shidan, ya zama na biyu a wannan bajintar a Premier tun bayan Islam Slimani a Disambar 2016 a wasan Leicester da Man City.

Trent Alexander-Arnold ya kara na uku a ragar Bournemouth kuma Firminho ne ya bashi kwalon, sannan dan wasan Brazil din ya zura na hudu tun kan hutu.

Virgil van Dijk ne ya ci na hudu, minti daya tsakani Chris Mepham ya ci gida, sai Roberto Firmino ya kara na biyu a wasan kuma na bakwai da Liverpool ta ci.

Kungiyar Anfield ta zura na takwas a raga ta hannun Fabio Carvalho, sannan Luis Diaz ya ci na tara a wasan.

Kwallon da Liverpool ta sharara da yawa a raga a Premier har da cin Rotherham Town 10-1 a shekarar 1896.

Liverpool ta fara yin 2-2 a gidan Fulham a gasar Premier ta bana, sannan ta yi 1-1 a Anfield da Crystal Palace ta kuma yi rashin nasara da ci 2-1 a hannun Manchester City.

Ranar 31 ga watan Agusta Liverpool za ta karbi bakuncin Newcastle United a wasa na biyar a Premier League.

Karo na hudu da aka ci kwallo tara a Premier League:

Liverpool 9-0 Bournemouth (2022)

Manchester United 9-0 Southampton (2021)

Leicester City 9-0 Southampton (2019)

Manchester United 9-0 Ipswich Town (1995)