Netherlands ta doke Afirka ta kudu a gasar cin kofin duniya

Netherlands

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Kasar Netherlands to doke Afirka da Kudu da ci 2-0 a wasan zagaye na biyu a gasar cin kofin duniya da aka buga a filin wasan Sydney.

Sakamakon na nufin tawagar ta kai wasan dab da na kusa da na karshe a gasar inda za ta kara da Sifaniya wadda a ranar Asabar ta lallasa Switzerland 5-1.

Yanzu Netherlands na neman yin nasara a wasanni biyu masu zuwa domin kai wa wasan karshe sau biyu a jere bayan ta yi hakan a gasar 2019 da aka gudanar a kasar Faransa.

Afirka ta Kudu na kan hanyar zuwa gida amma tabbas ta taka rawar gani a gasar ta bana, inda ta doke Italiya a wasanta na karshe a rukuni wanda ya ba ta damar tsallakawa zuwa zagaye na biyu wanda shi ne na farko a tarihinta.

Banyana banyana ta goga kafada da Netherlands duk da ta yi rashin Jermaine Seoposenwe da Bambanani Mbane sakamakon raunuka da suka samu kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Netherlands za ta koma kasar New Zealand don karawa da Sifaniya a Wellington ranar Juma'a.