Ƴar Masar ɗin da aka kama a Saudiyya kan yaɗa bidiyon batsa

Tala Safwan

Asalin hoton, TALA SAFWAN

Bayanan hoto, Tala Safwan ta yi fice a shafin Tiktok
An wallafa

An cafke fitacciyar 'yar kasar Masar din nan mai amfani da shafin TikTok a kasar Saudiyya kan zargin wallafa abubuwan batsa.

Tala Safwan na da mabiya miliyan biyar a shafin TikTok, da wasu 800,000 a shafin Youtube, kuma ta ja hankali ne bayan wallafa wani bidiyo da aka yi amfani da kalaman ‘yan madigo a ciki.

Sai dai Ms Safwan ta ce ba ta yi hakan da wata mummunar manufa ba. ‘Yan sanda a Saudiyya sun ce bidiyon ka iya cutar da wasu, da yada rashin tarbiyya.

Tala na jan hankalin matasa ma’abota shafukan sada zumunta da gajeren nannadadden bakin gashinta.

Bidiyon da take wallafawa na yawan tayar da kura a shafukan intanet, inda takan yi wa mabiyanta jawabi kan batutuwan da suka shafi soyayya da abubuwan da ba su dace ba.

Tana yawan yi wa mabiya shafinta barkwanci, da kokarin sanya su yin wani abu na nishadi da nufin ganin wanda ya fi yi daidai, kamar dai yadda aka san fitattun masu amfani da shafukan sada zumunta ke yi.

Sai dai a wannan karo, bidiyon da ta wallafa na aikewa da sako na daban.

Cikin takaitaccen bidiyon, an nuna Tala na hira da wata kawarta ‘yar Saudiyya, wadda ta gayyata gidanta.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wasu dai sun dauki maganganun da ta ke yi a bidiyon a matsayin na batsa.

Wannan ya sanya aka kaddamar da wani gangami a shafin Tuwita kan abin da ta yi, mai maudu’in "Tala ta bata wa jama’a rai."

Sai dai Tala ta mayar da martani da cewa ana yi mata mummunar fahimta, tare da musanta yin kalaman ‘yan madigo, wanda babban laifi ne dokokin kasar Saudiyya.

Ta kara da cewa an dan tsakuri wani bangare na cikakken bidiyon da ta yi, domin a shafa mata kashin kaji.

Yayin da batun ya ci gaba da ta da kura a shafukan sada zumunta, ‘yan sanda a birnin Riyadh sun ce sun kama wata ‘yar kasar da ta fito cikin bidiyo tana kalaman badala tare da wata mace, wanda hakan ka iya gurbata tarbiyya da ɓata wa jama’a zukata.

Sai dai ‘yan sandan ba su ambaci sunan Tala Safwan ba, amma sun wallafa sanarwa kan kamen da bidiyon da Tala ta yi da cikakkiyar fuskarta da kawarta.

Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan hukumar da ke sa ido a kan kafafen yada labarai ta Saudiyyar ta bukaci shafin YouTube ya cire tallace-tallacen da ba su dace da tarbiyya da koyarwar kasar ta Musulmai ba.

Hukumar ta yi barazanar daukar matakin shari’a matukar YouTube bai dauki mataki ba.

An fitar da sanarwar ce bayan korafin da iyaye suka yi kan ana yada abubuwan da ka iya gurbata wa ‘ya’yansu tarbiyya, cikin tallace-tallacen da YouTube ke yi.