Waiwaye: Ziyarar Sarauniya a Canada

An wallafa

Sarauniyar Ingila, Elizabeth II, wadda ta mutu ranar Alhamis 8 ga watan Satumban 2022 tana da shekara 96, tana da kyakkyawar dangataka da kasashen Turai.

Sarauniya Elizabeth II ta hau kan mulki ne shekara bakwai bayan Yakin Duniya na II.

A tsawon mulkinta na shekara 70, Sarauniyar ta yi tafiye-tafiye zuwa kasashe da dama na duniya.

A wannan bidiyon, an yi waiwaye ne kan ziyararta a kasar Canada, daya daga cikin kasashe rainon Ingila.