Martinez zai yi jinya har ƙarshen kaka

Lisandro Martinez lokacin da ya ji rauni

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Martinez ya ji rauni a wasansu da Palace a minti na 82 inda Matthijs De Ligt ya canje shi
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Ɗanbayan Manchester United Lisandro Martinez ba zai sake taka leda ba a sauran wasannin kakar nan saboda raunin da ya ji a guiwarsa, a ranar Lahadi.

An fitar da ɗanwasan ne mai shekara 27, a karawar da United ta yi rashin nasara a gida a hannun baƙinta Crystal Palace, raunin da tun a lokacin kociyan ƙungiyar Ruben Amorim ya bayyana a matsayin babbar matsala.

A ranar Alhamis ƙungiyar ta ce har yanzu ana duba yanayin raunin domin sanin yadda ya fi dacewa a yi masa magani da kuma tsawon lokacin da zai ɗauka yana jinya.

Sanarwar ta ce kowa a ƙungiyar yana yi wa Lisandro Martinez fatan warkewa sarai, kuma za su ci gaba da tallafa masa a kodayaushe.

Rashin Martinez babban ƙalubale ne ga Amorim wanda ke fama kan ganin ya dawo da ƙungiyar ta Old Trafford kan ganiyarta.

Yanzu United tana ta 13 a teburin Premier bayan kashin da ta sha a hannun Palace - rashin nasarar da shi ne na bakwai a wasa 13 na gida a bana.

A gobe Juma'a ne United za ta karɓi baƙuncin Leicester City, a karawar zagaye na huɗu ta cin kofin FA.

Martinez ya tafi jinyar ne yayin da United ɗin ke ɗari-ɗarin dawo na Luke Shaw, da ake ganin bai gama warkewa ba sarai, daga raunin da ya ji na ƙarshe.