Man Utd na son Gyokeres kan £80m, Diaz na kwaɗayin tafiya Barcelona

Viktor Gyokeres

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Manchester United na kokarin saye ɗan wasan gaba a Sweden, Viktor Gyokeres mai shekara 26, daga Sporting a wannan watan a kokarin ceto kanta a kakar bana, sai dai ana sa ran cinikin ya kai fam miliyan 80. (Mirror)

Real Madrid na kan gaba da saye Trent Alexander-Arnold a wannan kakar, inda matashin mai shekara 26 ke kokarin barin Liverpool. Ƙungiyar ta La Liga na son ɗan wasan na Ingila ya sanya hannu a kwantiragin wucin-gadi saboda kada ya sauya ra'ayi daga baya. (Relevo - in Spanish)

Amma Liverpool na son ci gaba da rike Alexander-Arnold har zuwa karshen kakar wasanni, wanda hakan zai sa Real Madrid ta yi kokari sake gwada sa'arta a watan Janairu. (Times - subscription required)

Burin daraktan wasannin Barcelona na gab da cika kan ɗan wasan Liverpool Luiz Diaz, bayan ɗan wasan na Liverpool mai shekara 27 ya nuna rashin jindadin soma tattauna sabon kwantiragin shi a Anfield. (Sport - in Spanish)

Arsenal ke kan gaba a gabatar da tayin saye ɗan wasan Eintracht na Frankfurt da Masar, Omar Marmoush mai shekara 25. Kungiyoyi irinsu Liverpool da Paris St-Germain da AC Milan duk na kwaɗayin ɗan wasan. (GiveMeSport)

Arsenal din dai na kuma son gwada sayen ɗan wasan Manchester United, Marcus Rashford, inda za ta gabatar da tayin da ya haura fam miliyan 25 kan ɗan wasan mai shekara 27 daga Ingila. (Football Transfers)

Rashford ya musanta tattaunawa da wakilai a yunkurin karkatar da su daga batun Manchester United a wannan watan. (MEN)

Fulham na fargabar ƙungiyar Marseille ta Faransa za ta sabunta zawarcinta kan ɗan wasan tsakiya a Brazil, Andreas Pereira, mai shekara 29. (Times - subscription required)

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Brentford da West Ham da Fulham na bibiyar ɗan wasan tsakiya a Crystal Palace mai shekara 29, Will Hughes. (Football Insider)

Bayern Munich da Paris St-Germain za su fafata da ƙungiyoyi firirmiya shida da ke son saye ɗan wasan gaba na Barcelona da Sifaniya, Dani Olmo, ko da yake har yanzu Barcelona ba ta hakura da yiwuwar yi masa rajista a zagaye na biyu na kakar bana ba. (Mirror)

Manchester United ta shirya gabatar da tayi kan ɗan wasan Brazil Casemiro da kuma mai buga tsakiya a Denmark Christian Eriksen, dukkaninsu na da shekara 32, da kuma ɗan wasan Sweden mai shekara 30, Victor Lindelof a watan Janairu. (Fabrizio Romano)

Athletic Bilbao na bibbiyar ɗan wasan Norwich City, Borja Sainz mai shekara 23, da ɗan wasan gefe a Sifaniya, Nico Williams mai shekara 22. (Sport via Football Espana)

Nottingham Forest za ta saurari tayin da aka gabatar mata kan ɗan wasan gaba daga Najeriya, Taiwo Awoniyi, mai shekara 27, a wannan watan, idan har akwai damar maye gurbinsa. (Mail - subscription required)

Kamfanin Adidas na Jamus zai soke kwantiragin fam miliyan 900 da ya cimma da Manchester United idan ƙungiyar ta Firimiya ta fadi a gasar. (Telegraph - subscription required)

Mai horas da 'yan wasa Ruben Amorim zai bai wa ɗan wasan Ingila mai shekara 17, Harry Amass da kuma mai buga tsakiya, Dan Gore, mai shekara 20, damar barin Manchester United a matsayin aro cikin watan Janairu. (Mirror)

Crystal Palace za ta yi kokarin daidaitawa da ɗan wasan Ingila mai shekara 25, Tyrick Mitchell a watan Janairu. (Football Insider)

Galatasaray na tattaunawa da Paris St-Germain a kan yarjejeniyar saye ɗan wasan Slovakia, Milan Skriniar mai shekara 29. (Florian Plettenberg)