Yanzu ne lokaci mafi dacewa da Arsenal za ta ci Champions League - Walcott

Theo Walcott

Asalin hoton, PA Media

Bayanan hoto, Theo Walcott ya taka wa Arsenal leda daga 2006 zuwa 2018 tare da cin ƙwallaye sama da 100
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Tsohon ɗanwasan gaba na Arsenal Theo Walcott ya ce yana ganin wannan ne lokaci mafi dacewa da ƙungiyar ta arewacin Landan za ta lashe gasar zakarun Turai ta Champions League.

Tsohon ɗanwansan na Ingila ya bayyana haka ne yayin da suke sharhi bayan wasan da Arsenal ɗin ta doke Real Madrid 2-1 a wasan zagayen kwata-fayinal ranar Laraba, inda ta fitar da ita daga gasar da ci 5-1 gida da waje.

Yanzu Arsenal za kara da PSG a zagayen kusa da na ƙarshe.

"Ina ganin wannan ne lokaci mafi dacewa su ci Champions League," in ji Walcott.

"Amma kuma fa za su kara ne da ƙungiyar da ke murmurewa tana ƙara kyau, kuma take a wurin da ya dace.

"Amma idan har za su iya doke Real Madrid, to za su iya cin kowa."

Karo na huɗu kenan da Arsenal ta kara da Real a Champions League, inda ta ci uku aka yi canjaras ɗaya.

A ranar 29 ga watan Afrilu Arsenal za ta karɓi bakuncin PSG a wasan farko, kafin a buga na biyu mako ɗaya bayan haka.

Arsenla ba taɓa cin kofin Champions League ba, kuma rabon da ta je wasan ƙarshe na gasar tun shekarar 2006 - lokacin da Barcelona ta doke domin lashe kofin.