Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ɗan Cristiano Ronaldo zai fara buga wa Portugal wasa
Portugal ta kira babban ɗan Cristiano Ronaldo domin fara buga mata ƙwallo a matakin ƴan ƙasa da shekara 15.
Cristiano Ronaldo Jr mai shekara 14 yana Al-Nassr a Saudiyya tare da mahaifinsa, inda yake taka leda tun Disamban 2022.
Kaftin ɗin na tawagar Portugal mai shekara 40 ya wallafa hoton ɗansa a tawagar ƙungiyar Portugal tare da saƙon cewa, "ina alfahari da kai, ɗana".
Ronaldo Jr zai buga wa Portugal wasa ne a gasar matasa da za a yi a Croatia tsakanin 13 zuwa 18 ga Mayu inda za su fafata da Japan da Girka da Ingila.
Kamar mahaifinsa, shi ma ya taka leda a Manchester United da Juventus da Real Madrid.
Ronaldo wanda ya lashe kyautar gwarzon ɗanwasan duniya ta Ballon d'Or sau biyar, har yanzu yana buga wa Portugal ƙwallo inda ya ci wa ƙasarsa ƙwallo 136 kuma wanda ya fi yawan cin ƙwallaye a tarihin ƙasar.
Ronaldo ya ci wa ƙasarsa kofin Turai a 2016 da kuma kofin ƙalubale na ƙasashe Nations League a 2019.
Tsohon ɗanwasan na Manchester United da Real Madrid da Juventus yana da wasu ƴaƴa huɗu - tagwaye Eva da Mateo da Alana Martina da kuma Bella.