Atletico Madrid za ta sallami Joao Felix, Marcos Alonso zai koma Manchester United

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Manchester United ta shaidawa ɗan wasan tsakiyar ta, ɗan asalin ƙasar Denmark, Christian Eriksen mai shekara 32 cewa zai iya barin ƙungiyar a watan nan. (Football Insider)

Manchester United ba ta da sha'awar shiga zawarcin ɗan wasan tsakiyar Barcelona da Netherland, Frenkie de Jong mai shekara 27, kuma ƙungiyar ta ce tana duba sauran zaɓin da ta ke da shi. (Metro)

Atletico Madrid na fatan za ta kammala sayar da ɗan wasan gaban ta, Joao Felix mai shekara 24, ga Chelsea, ta kuma ɗauko ɗan wasan tsakiyar Ingila mai shekara 24, Conor Gallagher, daga nan zuwa ranar Laraba. (AS - in Spanish)

AC Milan ta cimma yarjejeniya da Monaco a kan ɗan wasan tsakiyar Faransa mai shekara 25, Youssouf Fofana, wanda Manchester United ma ta ke zawarcin sa. (Sky Italy)

Stoke City da Swansea City da kuma Oxford United na gogayya da juna wajen neman sayen ɗan wasan Scotland mai shekara 20, Max Johnston daga Sturm Graz. (Football Insider)

Union Berlin da Getafe na kan gaba a zawarcin ɗan wasan gaban Ingila mai shekara 22, Cameron Archer, daga Aston Villa. (Fabrizio Romano)

Chelsea ta yiwa ɗan wasan tsakiyar Ingila mai shekara 22, Noni Madueke farashin £60m, ga duk wata ƙungiya da ke neman ɗaukar shi. (Athletic - subscription required)

Tsohon ɗan wasan bayan Chelsea da Sifaniya mai shekara 34, Marcos Alonso, ya ce yana fatan komawa Manchester United da taka leda idan kwangilarsa da Barcelona ta ƙare a baɗi. (Fabrizio Romano via Givemesport)

Paris St-Germain ta shirya shiga gaban Chelsea wajen neman ɗaukar ɗan wasan Rennes da kuma Fransa, mai shekara 23, Desire Doue. (ESPN)

Everton na tattauna yadda za ta ɗauki aron ɗan wasan tsakiyar Napoli mai shekara 25 daga Jens Castuje (TeamTalk)