Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Arsenal na tattaunawa da Sociedad kan Merino
Arsenal na tattaunawa da Real Sociedad kan yiwuwar sayen ɗan wasan tsakiya na Sifaniya Mikel Merino.
Merino na cikin tawagar Sifaniya da ta lashe gasar Euro 2024, kuma ya buga dula wasanni bakwai da ƙasar ta fafata a gasar, inda ya ci ƙwallo a wasan daf da na kusa da na ƙarshe da Sifaniya ta doke Jamus da ci 2-1.
Ɗan wasan mai shekara 28, na da sauran ƙasa da Shekara guda a kwantiraginsa da Sociedad wanda zai iya taimakawa Arsenal a yunƙurinta da ɗaukar ɗan wasan sakamakon zai iya fara tattaunawa da wasu ƙungiyoyi kan tafiya kan ƙyauta daga watan Junairu mai zuwa.
Abokin wasan Merino Martin Zubimendi ya ƙi amincewa da komawa Liverpool a farkon makon nan bayan ƙungiyar ta La Liga ta shawo kan ɗan wasan ya ci gaba da zama a kulob.
Idan Merino ya koma Arsenal, dan wasan tsakiya zai zama ƙarawa ƙungiyar ƙarfi a ɓangaren wasa ta sama, bayan ƙungiyar ta ɗauki ɗan wasan bayan Italiya Riccardo Calafiori a farkon wannan bazarar.
Merino ya taɓa wasa a gasar firimiya a baya, inda ya shafe shekara ɗaya a Newcastle kafin ya koma Sifaniya a shekarar 2018, yayin da ya taka leda tare da Odegaard a 2019-20 lokacin da ɗan ƙasar Norway ɗin ya yi zaman a aro a Sociedad daga Real Madrid.
Merino ya buga wasanni 45 a dukkan gasa a kakar wasan data gabata inda ya zura ƙwallaye takwas.