Waiwaye : Gayyatar Wike zuwa APC da Warin gawarwaki a Mokwa
Wannan maƙala ce da ke kawo muku muhimman batutuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi.
Muna kira ga Tinubu ya mayar da hankali kan gyaran Najeriya ba zaɓen 2027 ba - ACF

Asalin hoton, Bayo/X
A ranar Litinin da ta gabata ne ƙungiyar Tuntuɓar Juna ta Arewacin Najeriya ta yi kira ga Shugaba Tinubu da manyan muƙarraban gwamnatinsa da su mayar da hankali wajen ganin sun kyautata rayuwar ƴan Najeriya maimakon gangamin yaƙin neman a sake zaɓen Tinubu a 2027.
A wata sanarwa da kakakin ƙungiyar, Farfesa Tukur Muhammad-Baba ya fitar kungiyar ta ce, yin hakan ya yi wuri.
Sannan ƙungiyar ta taya Musulmi murnar Babbar Sallah.
Ƙungiyar ta bayyana rashin jin daɗinta dangane da taɓarɓarewar tsaro da tsadar rayuwa da rashin wutar lantarki da matsalolin lafiya, da ilimi da karyewar darajar Naira da tashin farashin kayan abinci.
Ƙungiyar ta kuma nuna takaicinta da cewa duk da irin waɗannan ƙalubale, jam'iyyar APC mai mulki ta fi mayar da hankali kan gangamin yaƙin neman zaɓen Tinubun a 2027.
Masu ƙwacen waya sun kashe babban soja a Kaduna

Asalin hoton, OTHERS
A ranar Lahadin makon da ya gabata ne, wani mai ƙwacen waya ya kashe wani babban soja bayan da ya nemi ya miƙa masa wayar da ke hannunsa.
Wata sanarwa da rundunar sojin Div 1 da ke Kaduna ta fitar ta ce Lt Commodre M Buba da ke kwas na shiga layin manyan sojoji ya samu fanco a tayar motarsa abin da ya tilasta masa tsayawa a daidai gadar sama ta Kawo da ke Kaduna, inda fitowarsa ke dawuya sai wani ya zo ya same shi ya nemi ya ba shi wayarsa.
Sai sojan ya nemi sanin dalilin bayar da wayar abin da ya sa mutumin ya fitar da wuƙa ya caka masa a ƙirji.
Wani ɗan sintiri ya yi ƙoƙarin ceton sojan amma shi ma mutum ya daɓa masa wuƙar a hannunsa.
An kai Lt Commodore asibitin Manalal amma kuma rai ya yi halinsa.
Sai dai kuma mutanen da ke kusa da wurin da abin ya faru sun yi wa makashin tara-tara inda suka hallaka shi shi ma.
Za a samu raguwar mace-macen mata masu juna biyu da kashi 20 cikin dari nan da 2027 - Gwamnatin Najeriya

Asalin hoton, Google
Gwamnatin Najeriya ta ce akwai yiwuwar za a samu raguwar mace-macen mata masu juna biyu a yayin haihuwa da kashi 20 cikin ɗari kafin nan da shekarar 2027.
Ƙaramin ministan Lafiyar Najeriya Iziaq Salako ne ya bayyana hakan, a ranar Litinin da ta gabata inda ya ce gwamnatin ƙasar na kuma ƙokarin cimma muradin ganin an samu raguwar mutuwar jarirai da yara ƴan ƙasa da shekara biyar da kimanin kashi 15 cikin ɗari.
Gwamnatin ta bayyana matakai daban-daban da za su taimaka wajen cimma hakan kamar samar da kayan aiki, da horo ga Jam'ian lafiya.
Najeriya dai ƙasa ce da aka fi samun mace-macen mata masu juna biyu a duniya, kamar yadda wani bincike da BBC ta gudanar ya tabbatar.
Tinubu ya gayyaci Wike zuwa APC

Asalin hoton, Nyesom Wike/Bola Tinubu
A ranar Larabar da ta wuce ne Shugaba Bola Tinubu ya gayyaci ministan Abuja, Nyesom Wike, da ya shiga jam'iyyarsu ta APC, a cewarsa, bisa la'akari da irin ayykan alheri da yake yi a babban birnin.
Tinubu ya miƙa wa ministan, wanda dan babbar jam'iyyar hamayya ta PDP ne, goron gayyatar ne a lokacin ƙaddamar da tituna a Abuja, yana mai cewa a shirye suke su karbe shi a duk lokacin da ya yanke shawarar sauya sheƙa.
Tinubu ya ce Wike na aiki tuƙuru a gwamnatin APC duk kuwa da cewa shi ba mamba ba ne a jam'iyyar.
Nyesom Wike dai ɗan jam'iyyar PDP ne kuma ya ce babu inda zai je duk da halin rikicin cikin gida da jam'iyyar ke fama da shi a yanzu haka.
Alummar garin Mokwa na fargabar ɓarkewar cutuka saboda gawarwakin da ba a gano ba

Asalin hoton, OTHERS
Aƙalla makonni biyu da afkuwar ambaliyar ruwan da ta hallaka mutane tare da share gidaje masu dimbin yawa a garin Mokwa na jihar Neja, jama'ar yankin na kokawa kan yadda aka soma jin warin gawarwakin mutanen da har kawo yanzu ba a kai ga ganowa ba.
A ranar Laraba ta makon jiya ne wasu daga cikin al'ummar garin suka koka da hakan inda suka bayyana cewa warin na iya haifar da matsala ga lafiya, musamman ana fargabar barkewar kwalara kasancewar da dama daga rijiyoyin jama'a da suke samun ruwan sha sun rufta.
Daga cikin wadanda BBC ta zanta da su, sun ce tun daga ranar asabar ta karshen makon daya gabata suka soma jin warin gawarwakin.
Ina jin daɗin ganin jam'iyyun hamayya cikin matsala - Tinubu

Asalin hoton, BOLA TINUBU
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce yana farin ciki da halin rikici da jam'iyyun hamayya da dama na ƙasar ke ciki.
Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin jawabin da ya yi na ranar tunawa da dimokuraɗiyya a zauren majalisar dokokin ƙasar da ke Abuja, a ranar Alhamis da ta wuce.
"Ina jin daɗin ganin jam'iyyun hamayya a tagayyare," kamar yadda shugaban ƙasar ya bayyana a jawabinsa na ranar dimokuraɗiyya.
Tinubu ya ce "ba zan ce ina so na ga kun gyaru ba, ina ma jin dadin ganinku a haka.
Tinubu ya ce jam'iyyar APC ba za ta hana kowa shiga cikinta ba domin yin hakan tauye hakkin al'umma ne.
Masu zanga-zanga sun fito a biranen Najeriya

Asalin hoton, OTHERS
Harwayau a ranar Alhamis din da ta gabata ne, ranar bikin dimukuradiyyar ta Najeriya, masu zanga-zanga suka fito a biranen kasar domin kokawa kan halin da ƙasar ke ciki.
Daga cikin abin da masu zanga-zangar ke kokawa a kai akwai talauci da matsin rayuwa, waɗanda suke zargin manufofin gwamnati sun haifar.
Haka nan masu zanga-zangar na kokawa kan rashin tsaro wanda ke addabar yankuna da dama na ƙasar.
Cire tallafin man fetur da sauye-sauye a ɓangaren kudi sun haifar da tashin farashin kayan masarufi da faduwar darajar kudin ƙasar, kamar yadda masana suka bayyana.
Sai dai gwamnatin ƙasar ta ce manufofin nata za su yi amfani a nan gaba.











