Yadda ƙwallo ke haɗa kan ƴan Najeriya, su manta da damuwarsu

    • Marubuci, Nabeela Mukhtar Uba
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Broadcast Journalist
    • Aiko rahoto daga, Abuja
  • An wallafa

Idan akwai wani abu guda ɗaya da ke haɗa kan ƴan Najeriya mai yawan ƙabilu da addinai shi ne ƙwallon ƙafa.

A ƙwallon ƙafa ne za ka ga ƴan Najeriya a ƙarƙashin inuwa guda suna kallo tare, suna murna tare idan aka yi nasara, suna takaici idan aka samu akasi.

Yanayin kan sa ƴan Najeriya da ke fama da gomman matsalolin ƙunci da tsadar rayuwa da rashin tsaro su manta damuwar da suke ciki.

Wannan haɗin kan aka gani bayan wasan Najeriya da Afirka ta Kudu a zagayen kusa da na ƙarshe a gasar cin kofin Afirka da ke gudana a Ivory Coast wasan da yanzu ya bai wa Super Eagles damar zuwa zagayen ƙarshe na gasar inda za ta fafata da Ivory Coast mai masaukin baƙi, ranar Lahadi.

Ko gabanin wasan - fatan nasara ga Super Eagles za ka yi ta gani a shafukan sada zumunta - mutane sun jingine damuwarsu sun koma yi wa ƙasarsu kyakkyawan fata a wasan.

Bari na tsakuro wasu saƙonni da ƴan Najeriya suka riƙa wallafawa a shafin X bayan da Najeriya ta yi nasara a wasanta.

Obiasogu David, wani dan Najeriya ne wanda a sakonsa ya ce "Na ji dadin yadda Ahmed Musa ke samun yabo saboda jajircewarsa wajen karfafa wa 'yan wasan Super Eagles gwiwa daga benchi.

Tun farko lokacin da aka kalubalanci yadda aka sa shi cikin tawagar, ya ce ba ƴan wasan da ke filin wasa ne kaɗai ke cin wasa ba, ƙwarin gwiwar da suke samu daga benci na taka muhimmiyar rawa - akwai jagorancin da tsofaffin 'yan wasa ke ba su daga benci." in ji David

Shi ma Prince Adeshina ya wallafa wani bidiyo ne a shafinsa na X da ke nuna mara lafiya yana kallon wasan Super Eagles da Bafana Bafana yana rike da sandar sakala ledar karin ruwa.

Wannan ya nuna duk da halin jinya da yake ciki amma hakan bai hana shi kallon wasan ba.

Farfesa Isa Pantami, ministan sadarwa a mulkin shugaba Muhammadu Buhari, shi ma ya wallafa wani bidiyo a shafinsa na X dauke da sakon "yanzu jirginmu ya sauka, babu sadarwar intanet, yadda 'yan Najeriya da ke jirgin suke cikin zulumi saboda rashin sanin sakamakon wasan Najeriya da Afirka ta Kudu a #AFCON2023. Irin murnar abin burgewa ne kuma hadin kai a Najeriya abu ne mai yiwuwa."

Ko me ya sa ƙwallo ke haɗa kan ƴan Najeriya?

Bashir Hayatu Gentile, mai sharhi ne a harkar wasa kuma ya shaida wa BBC cewa kwallo tana da wani babban sirri a cikinta da yake sa 'yan Najeriya hadewa a duk lokacin da ake yin ta.

Ya ba da misalin cewa "za ka ga watakila akwai wani a ciki shahararre dan bangarenka ne, kamar Stephen Keshi (lokacin da yake kyaftin din Najeriya), wanda yake kudu maso gabashin Najeriya zai ga cewa ai kyaftin din kasarmu ma namu ne." in ji Gentile.

"Idan ka dawo bangaren Yarabawa, za ka ga Monday Odiaka wanda dan Legas ne kuma duk wani dan kasar Yarabawa zai ji bari na goyi bayan sa, mu zamanin da muka zo a arewacin Najeriya, ai dalilin Tijjani Babangida da Garba Lawal da Daniel Amokachi, yan arewacin Najeriya sun ba wa yan Najeriya gudummawa."

Ya ce ko a wasan da Super Eagles ta doke Bafana Bafana na ranar Laraba, an samu wasu dandazon magoya bayan golan Najeriya Stanley Nwabali (wanda ya yi nasarar tunkude kwallo biyu a bugun daga kai sai mai tsaron raga) da suka yi tattaki zuwa gidan mahaifinsa inda suke kade-kade cikin murna da shewa.

"Wannan ya nuna ana goyan bayan kulob din ne saboda mutane suna kallon wakilansu ne a cikin wadan nan wasannin." in ji masanin.

Yadda ƙwallo take haɗa kan jama'a

Bashir Hayatu Gentile ya ce kwallo ta zama kamar wata gada tsakanin kabilu ko addini a kasa.

"Ana amfani da ita wajen samun yancin kai ko raba rigingimu, kamar a Najeriya duk sanda za a yi bal, ba a maganar addini ko bangaranci, haduwa ake yi da kowace irin kabila da kowane irin addini." A cewarsa.

Ya ba da misali da shekara 27 da suka gabata da Najeriya ta samu kyautar zinare bayan da ta doke Argentina a wasan Olympics na 1996.

Ya ce a lokacin gwamnatin Abacha tana cikin tsanani wani bangare na Najeriya na rigima da ita "amma dalilin dauko wannan kyauta, ya zamana cewa ana kiran Abacha, saboda shi ne shugaba, mutane sun manta tsananin."

"Haka lokacin da aka yi yakin basasa a Najeriya , an yi kokari an kafa manyan kulob-kulob a kowane yanki na kasar." in ji masanin.

A cewarsa, irin haka yana kawo hadin kai da kyakkyawar fahimta domin kowa yana "komawa cewa kasata ce take yi, wannan kishin kasar ne yake sa a tafi a alkibla daya, bangare daya a goyi bayan mutane.

Ya ce irin haka ya faru a Ivory Coast da a yanzu take karbar bakuncin gasar lokacin da ake yakin basasa a kasar "ana ta yaki tsakanin arewaci da kudancin Cote D'Ivoire, Didier Drogba shi ya hada kan yan bal da suke wasa a duniya irinsu Kole Toure da dan uwansa.

"Sun je suka yi bal a Bouake inda nan ne cibiyar yan adawa, an tashi daga bal din ya durkusa a filin wasan ya ce yana rokon yan tawaye su zo a hadu a gina kasa, daga nan aka daina duk wani yakin basasa a Cote D'Ivore."

Wannan a cewarsa, yana nuna yadda kwallo ke hada yan kasa, ana ajiye banbance-banbancen addini ko na kabilanci.

Rawar da ƴan ƙwallo za su iya takawa a ɓangaren tsaro

A bayanin da ya yi, Gentile ya ce ana iya kwaikwayon irin yadda kwallo take hada kan jama'a wajen samun nasara a matsalolin da ake fuskanta.

Ya ce game da matsalolin tsaro, ana iya tattara yan kwallon da ake da su, a zagaya da su fanni-fanni su yi kira ga mutane da shugabannin addini da yan siyasa da sarakuna.

"Za a iya zuwa wajen Sarkin Musulmi da wajen Oba na Legas da malamin darikar Tijjaniya ko na izala ko sanatoci da yan majalisar wakilai, a yi kungiya a je wajen shugaba Tinubu a ce mu yan bal da muke bugawa Najeriya muna son a yi kaza a bar kaza." in ji Bashir Gentile.

Ya ce yan wasan kwallo suna taka rawa sosai wajen samun zaman lafiya a kasa, "an yi a Saliyo da Liberiya.