Masu maulidi da gasar sarauniyar kyau a Najeriya cikin hotunan Afrika

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Wasu daga cikin zaɓaɓɓun hotunan Afirka da na ƴan nahiyar a wasu sassan duniya

Sarauniyar Kyau

Asalin hoton, Emmanuel Adegboye / EPA

Bayanan hoto, Ɗaya daga cikin waɗanda suka shiga gasar Sarauniyar Kyau ta Najeriya a ranar Asabar
Wata mai shiga gasar Sarauniyar Kyau a Najeriya

Asalin hoton, Emmanuel Adegboye / EPA

Bayanan hoto, Gasar ta Sarauniyar Kyau ta Najeriya ta yi zafi yayin da kowa ya dage don yin nasara
Sarauniyar da ta yi nasara

Asalin hoton, Benson Ibeabuchi / AFP

Bayanan hoto, A ƙarshe dai, Chidimma Adetshina, wadda ta yi nasara a gasar Afirka ta Kudu amma aka nuna mata wariya, ita ce ta zama Sarauniyar ta Najeriya
Giwa

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Wata giwa da aka yi shekaru ana wasa da ita mai suna Charley, a sabon gandun dajin da aka dawo da ita, bayan yi mata ritaya a Limpop da ke Afirka ta Kudu
Yara rike da tutoci

Asalin hoton, Andres Martinez Casares / Reuters

Bayanan hoto, Yara a China na ɗauke da tutocin ƙasarsu da na ƙasashen Afirka, domin maraba da shugabannin Afirka da suka halarci taro a Beijing
Makada a China

Asalin hoton, VCG / Getty Images

Bayanan hoto, Makaɗa sun ƙayatar da mahalarta taron ƙolin na China da Afirka
'Yan wasa na murna

Asalin hoton, Franck Fife / AFP

Bayanan hoto, Ƴar gasar tseren mita 400 ta mata Lahja Ishitile, ta Namibia na murna tare da jagoranta bayan ta yi nasara a gasar Olympic ta masu naƙasa ta Paris 2024
Wata mata da 'yarsanda

Asalin hoton, Abubaker Lubowa/ Reuters

Bayanan hoto, Ƴarsanda a Uganda ta tsare wata mata da ta shiga zanga-zangar mata tsirara a kan cin hanci da rashawa a kofar majalisar dokokin ƙasar a Kampala
Masu wasan gargajiya

Asalin hoton, Emmanuel Croset / AFP

Bayanan hoto, Dakarun masarautar Eswatini - Mulukiyar Afirka ta ƙarshe, sanye da kayan wasan gargajiya a fadar Sarkin, da ke Ludzidzini.
Masu Maulidi

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ranar Laraba ke nan a wani titi a Gadaref da ke Sudan, inda Musulmi ke bikin Maulidin Annabi Muhammad (SAW)