Me ke haddasa sanƙo kuma ta yaya za a kauce masa?

A man checking his hair in the mirror

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sano matsala ce da ake dangantawa da gado
    • Marubuci, Ameer Ahmed
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Zubewar gashi kan faru da kowa, ba tare da la'akari da jinsi ko shekaru da ƙabila ba.

Za ka iya fara rasa gashin kanka saboda wasu dalilai masu yawa, da suka haɗa da na gado ko sharain magani ko ma yanayin yadda kake gudanar da rayuwarka.

Domin gano dalilai da kuma magance sanƙo, mun yi magana da Enitan Agidee, daraktan a wata cibiyar kula da gashi da sanƙo da ke Birtaniya, kuma likitar da ke duba masu lalurar sano musamman mata.

"Babu wanda ba ya fuskantar matsalar sanƙo, har ni wadda nake da masaniya kan abin da ya shafi gashi na fuskanci matsalar sanƙo a baya,'' in ji ta.

Mujallar 'Dermatologic Surgery' ta Amurka ta bayyana cewa kashi 16 na maza masu shekara 18 zuwa 29 na fuskantar sanƙo, yayin da kashi 30 na masu shekara 30 zuwa 39 ke ɗauke da sanko, sannan fiye da kashi 50 cikin 100 na masu shekara 40 zuwa 49 na ɗauke da matsalar.

Maza sun fi mayar da hankali kan amtsalar sanƙo, to amma mata da dama na fuskantar matsalar.

Makarantar Kiwon Lafiya ta Havard ta ce kusan kashi ɗaya bisa uku na mata kan fuskanci sanƙo a wani mataki na rayuwarsu.

Abubuwan da ke janyo sanƙo

Ana yi wa wata mata kitso a shagon gyaran gashi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Enitan Agidee, wata mai kula da gashi ta ce nau'in gyaran gashin da ake yi wa mata kan taimaka wajen haddasa sanƙo

Sanin nau'in gashinka na da matuƙar muhimmanci.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Enitan Agidee ƙwararriya kan gashi, ta ce wasu nau'ikan gyaran gashi da mata ke yi kamar ɗaure shi ko manya-manyan dogayen kitso ko ƙone shi a wasu lokutan kan haifar da sanƙo.

"Gane irin nau'in gyaran gashin zai taimaka wajen magance matsalar. Za ki iya yin yadda kika ga dama da gashinki, amma yana da kyau ki san yaushe ya kamata ki yi nau'in gyaran gashin da kike buƙata, musamman masu nauyi da wanda ake ɗaure gashin da ƙarfi, za su iya haddasa miki sanƙo,'' a cewarta.

Maɓuɓɓugar gashin shi ke taimaka wa gashin girma idan ya tsiro, kuma shi ke taimakawa wajen warkar da ciwo da raunukan da suka shafi fata a fatar kanku.

Wasu ƙarin abubuwan da ke haddasa ko ta'azzara sanƙo shi ne shan taba ko basara, da gajiya da kuma rashin wadataccen bacci.

Dakta Pantha ta ce shan taba kan haifar da wani yanayi da ke rage kwararar jini zuwa sauran sassan jiki, kuma hakan zai shafi fatar ka, inda gashin ke fitowa.

Haka ma yawan wanke fatar a kodayaushe kan haddasa zubewar gashi, za ku fahimci haka idan kuna wanke kanku, za ku ga gashi na faɗowa daga kanku, koda kuwa ba ku yi shamfo ba.

Danka Panth ta bayar da shawarar cewa ''idan fatar kanku ba mai maiko ba ce za ku iya wanke kanku sau guda a kowace rana, koma sau ɗaya a cikin kwana biyu''.

To amma ta ce idan fatar kanku tana bushewa da wuri, to za ku iya wanke kanku a ƙalla sau uku a kowane mako.

Ta yaya za ka dakatar da sanƙo idan ya fara bayyana?

Wata mace ke duba gashinta a madubi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A wasu lokutan matsalar sanƙo kan ragu sakamakon amfani da wasu magunguna, amma masana sun ce matsala ce mai alaƙa da rayuwa.

Abu na farko da za ka yi shi ne ganin ƙwararren likita, in ji Dakta Aanchal panth ƙwararriyar likitar fata, tana mai cewa akwai sauye-sauyen da mutum zai yi a rayuwarsa ta yau da kullum.

"Cin abinci mai gina jiki zai taimaka wajen tohowar gashi,'' in ji ta.

Ta ƙara da cewa idan akwai matsalar abinci mai gina jiki, to abu na farko da ya kamata ka yi shi ne magance wannan matsalar.

Mutane da dama da suka gano cewa gashinsu na zubewa, sukan yi amfani da wasu mayukan shafawa masu ɗauke da sinadari, kamar masu ɗauke da sinadaran minoxidil, ko caffeine.

Galibi mayukan Minoxidil kan zo a nau'in ruwa ko man shafawa. Yakan taimaka wajen ƙara yadda zai riƙa zagayawa har zuwa tushen gashi, wanda kuma zai taimaka wajen gashin ya yi tsawo sosai.

Haka kuma Dakta Panth ta yi gargaɗin cewa man na minoxidil ''zai taimaka wajen kaurara gashi, amma ba wani sabon gashi ne zai toho ba''.

Musamman ga maza, sukan yi amfani da man ketoconazole domin magance matsalar sanƙo.

Masana sun ce wannan zai taimaka wajen magance matsalar amosanin ka, saboda tana ɗaya daga cikin abubuwan da ke tsananta da sanƙo.

Saɓanin minoxidil, ketoconazole na magani ƙwayoyin cuta na fungal da ake samu a ka.

Wasu binciken da ake yi sun nuna cewa maganin na ketoconazole ka iya rage yawan sinadarin DHT mai alaƙa da sanƙo.

"Mutane da dama na jin cewa sanƙo wani abu ne da za ka iya shan magani, kuma gashin zai tsiro, amma ba haka ba ne. Dawo da gashi kamar wani abu ne da duk mai sanƙo yake so,'' in ji Panth.

Dashen gashi ka iya zama mafita?

Wani mutum bayan yi masa dashen gashi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kusan mutum miliyan guda ne suka je Turkiyya a shekarar da ta gabata domin yin dashen gashi a cewar wata ƙungiya da ke kula da masu yawon buɗe ido a ƙasar.

Dashen gashi wani nau'in tiyata ne da ake yi domin magance matsalar sanƙoc, da dawo da gashinsu da ya zube.

In banda tsadar hanyar, dashen gashi fitaccen abu ne da zai dawo maka da ainihin gashinka da ya zube, a cewar Dakta Panth.

To sai dai ta ce, abin da mutane ba su fahimta ba game da dashen gashi, shi ne idan ka daina shan maganin sanƙo, bayan dashen, to a cikin shekara biyar zuwa shida sauran gashin naka da ya rage duka zai ragu ya barka da wanda da yi dashen.

Trichologist Enitan Agidee na ganin cewa dashen gashi ne hanya ta ƙarshe da mutum zai runguma idan duka sauran hanyoyin magani ba su yi masa aiki ba, kuma ita ma hanyar ba kowa take yi wa kyau ba.

"Dashen gashi tamkar mutum ne ana tsananin sanyi ya saka rigar sanyi amma bai zuge zif ba....''

"Kana fita waje za ka fara jin sanyin."