Mene ne tuddan Golan kuma me Israila ke yi a wurin?

Motocin sojojin Israila suna shiga ƙofa da ke  wata katanga a yayin da suka dawo daga yankin tudun mun tsira daga Syria da ke kusa da ƙauyen Druze na Majdal Shams.

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Jeremy Howell
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 7

Dakarun Israila sun ƙwace ikon tudun mun tsira inda ba sojoji a ciki, da ke kan tuddan Golan, da kuma wasu wurare da dama da ke yankin Syria.

Firaministan Israila Benjamin Netanyahu ya ce matakin wucingadi ne domin tsare Israila daga harin ƴantawayen Syria sakamakon rugujewar gwamnatin Bashar al-Assad.

Bayan haka, gwamnatin Israila ta amince da wani tsarin da zai ƙarfafa wa mutane samun wurin zama a kan tuddan Golan.

ƙasashen Larabawa da dama sun yi allawadai da ƙwace yankin da Israila ta yi.

Ina ne tuddan Golan kuma wa ke da iko da su?

Tuddan Golan wuri ne mai cike da duwatsu da ke kudu maso yammacin Syria, da ya haɗa har zuwa arewa maso gabashin Israila. Yankin na ƙarƙashin mamayar sojojin Israila.

A yaƙin kwana shida na shekarar 1967, Syria ta kai wa Israila hari kan tuddan, sai dai Israilar ta mayar da martani kuma ta ƙwace aƙalla faɗin murabba'in ƙasa 1200 na yankin.

Syria ta yi ƙoƙarin ƙwato tuddan Golan din a lokacin yaƙin gabas ta tsakiya na 1973, amma ta gaza.

Ƙasashen biyu sun sanya hannu kan yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin duniya na farko na 1974, wanda ya buƘaci rundunonin su fice zuwa kowane gefe na zirin ƙasa mai tsawon kilomita 80, wanda ake kira 'tudun mun tsira" a kan tuddan, kuma wani rukuni na Majalisar Ɗinkin Duniya da ake kira dakarun sanya ido, suna yankin tun a lokacin domin sa ido kan bin yarjejeniyar.

A shekarar 1981, Israila ta mamaye yankin tuddan Golan, kuma mutane suka fara gina gidajensu a wurin.

Ba a la'akari da yancin Israila kan yankin a duniya, Amurka ce kawai ke yi.

Gwamnatin tsohon shugaba Donald Trump ce ta karya tsarin Amurka na gwamman shekaru ta yin hakan a shekarar 2019.

Syria ta ce ba za ta yi wata yarjejeniyar zaman lafiya da Israila ba, har sai ta janye daga Golan gabaɗaya.

A watan Nuwamban 2024, Israila ta karbi ƙorafe-ƙorafe daga Syria da Majalisar Ɗinkin Duniya kan gina ramuka a gefen tudun mun tsira, wanda daga bisani ya tsallako zuwa cikin tudun mun tsiran.

Me ya sa tuddan Golan ke da muhimmanci?

Ana iya gano Syria daga saman tuddan Golan.

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Syria ta yi amfani da manyan makamai a lokuta da dama domin kai hari kan arewacin Israila daga 1948 zuwa 1967 a lokacin da take iko da tuddan Golan.

Wuri mafi tsawo a yankin shi ne tsaunin Hermon, wato Jabal al-Shaykh a Larabci, wanda yake da tsawon mita 2,814 daga teku.

Babban birnin Syria, Damascus, wanda ke da nisan kilomita 60 a arewa, ana iya hango shi daga kololuwar tsaunin a ranakun da babu hazo, tare da wani yankin kudancin Syria.

Yin iko da yankin zai bai wa Israila babbar dama ta sanya ido kan ayyukan sojojin Syria, da idanu ko kuma da na'ura.

Gangaren da ke kai wa zuwa ga tsaunin yana kuma taimaka wa Israila a matsayin wata kariya kan hari daga sojojin Syria, kamar yadda aka yi a yaƙin 1973.

Tuddan Golan wani muhimmin hanya ce ta samun ruwa a yankin da bai da wadatar ruwan sama.

Ruwan sama daga tsaunin na shiga cikin kogin Jordan, wanda hakan ya sa ƙasar da ke yankin ke da albarka da za a iya shuka inibi da sauran kayan abinci, kuma ya samar da abinci ga shanu.

Ɗaya daga cikin manyan abubuwan da suke kawo tsaiko wajen yin yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Israila da Syria shi ne bukatar Syria Ta ficewar Israila gaba ɗaya zuwa iyakarta kafin shekarar 1967.

Hakan zai bai wa Syria damar yin iko da gaɓar tekun Galilee, waɗanda 'yan Israila ke kira Tafkin Kinneret, Larabawa kuma suke kiran shi tafkin Tiberius, wanda zai daƙile wa Israila hanyar samun ruwa.

Israila kuma ta ce ya kamata a saka iyaƙar a gabashi.

Ra'ayoyin al'umma a Israila na nuna suna so a ci gaba da riƙe tuddan Golan, inda wasu mutanen ke ganin yankin na da muhimmanci da amfani sosai da bai kamata ace an mayar da shi ba.

Wa ke zama a tuddan Golan?

Wani mazaunin ƴanIsraila mai suna Katsrin a yankin da ta mamaye da ke tuddan Golan.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Da yawan wadanda suke wurin har yanzu da aka ƙiyasta yawansu ya kai 20,000, ƴan darikar Druze ne

Akasarin ƴan Syria da ke rayuwa a tuddan Golan sun tsere daga yankin a lokacin yaƙin 1967.

Da yawan waɗanda suke wurin har yanzu da aka ƙiyasta yawansu ya kai 20,000, ƴan darikar Druze ne.

A yanzu haka akwai fiye da garuruwa 30 na ƴan Israila a yankin Golan, wanda mazauni ne ga akalla mutane 20,000. 'Yan Israilan sun fara gina shi ba tare da wani jinkiri ba a ƙarshen yaƙin 1967.

Ana kallon mazaunin a matsayin wanda ya saɓa doka a ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa, sai dai Israila ta musanta hakan.

Bayan mamayar da Israila ta yi a yankin tudun mun tsira da ke tuddan Golan, Netanyahu ya ce yana so adadin mutanen da ke zaune a wurin ya ninka yadda yake a yanzu.

Ya ce Israila za ta ci gaba da riƙe yankin, ta bunƙasa shi, ta kuma zauna a ciki.

Syria ta ce a tarihi tuddan Golan nata ne, kuma ta sha alwashin ƙwato yankin, yayin da Israila ke cewa tsaunin na da matuƙar muhimmanci ga tsaronta kuma zai kasance a wurinta har abada.

Me Israila ta yi a tuddan Golan a baya-bayan nan?

Wata motar yaƙi na Israila na shiga Quneitra, wani gari da mafi yawan shi babu mutane a kan tuddan Golan.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wata motar yaƙi ta Israila na shiga Quneitra da ke Tuddan Golan.

Rundunar sojin Israila IDF sun ƙwace ikon tudun mun tsiran da ba a aikin soji a ciki da ke tuddan Golan, bayan sojojin Syria sun bar gurin da suke aiki a yankin sakamakon gabatowar da dakarun ƴan tawaye ke yi.

Kwamandojin IDF sun kuma ce ayyukan sojojinsu suna wuce tudun mun tsira da ke tuddan Golan.

Netanyahu ya ce dakarunsa suna kafa wata matsayar kare kai ta wucingadi gabanin a samar da yarjejeniyar da ta dace.

'' Idan za mu iya samar da alaƙa ta maƙotaka da kuma alaƙa ta zaman lafiya da sabbin dakarun da ke fitowa a Syria, haka muke sha'awa. Amma idan hakan bai samu ba, za mu yi duk mai yiwuwa wajen kare Israila da kare iyakar Israila.'' a cewar shi.

Duk da iƙirarin da Israila take yi na cewa ƙwace tudun mun tsiran na wucin gadi ne, minstan tsaron ƙasar Isreal Katz, ya ce dakarunta da ke kan tsaunin Hermon wajibi ne su shirya zama a wurin har ƙarshen hunturu.

A cikin wata sanarwa, Mr Katz ya ce: '' sakamakon abun da ke faruwa a Syria, akwai muhimmancin tsaro sosai mu ci gaba da riƙe ƙololuwar tsaunin Hermon, kuma dole a yi duk abin da za a iya domin tabbatar da shirin IDF a yankin domin taimaka wa sojojin zama a wurin a cikin yanayi mai wahala.

Ƙasashen Larabawa da dama sun soki matakan Israila.

Ministan harkokin ƙasashen wajen Masar ya bayyana matakin a matsayin ''mamayar yankin Syria da kuma saɓa yarjejeniyar 1974.''

Netanyahu ya ce ya ɗauki matakin kare iyakar Israila ne saboda a cewarsa, bayan ƙwace ikon Syria da ƴan tawaye suka yi, yarjejeniyar 1974 ta rushe.

Sai dai Farfesa Yossi Mekelberg na Chatham House, wata cibiyar bincike kan harkokin ƙasa da ƙasa da ke London, ya ce Syria ba ta ce ba za ta bi ƙaidojin yarjejeniyar ba.

'' Wannan ɗaukar mataki kafin faruwar abu ne da Israila ta yi domin tabbatar da tsaronta, amma babu buƙatar ayyukan sojoji.

Akasarin masu fashin baƙi suna da shakku kan halasta ɗaukar matakin da Israila ta yi.

Dakta HA Hellyer daga makarantar Royal United Services, wata cibiyar bincike da ke Birtaniya ya ce babu yiwuwar ƙungiyoyin tawayen Syria za su yi ƙoƙarin ƙwace tuddan Golan a nan kusa.

''Al'amuran cikin gida za su ɗauke musu hankali gabaɗaya da ba za su yi tunanin ƙirƙiro sabon rikici da Israila ba'' inji shi.

Farfesa Mekelberg ya ce mamayar Syria da Israila ta yi za ta lalata alaƙar gwamnatocin nan gaba a yankin: '' yadda Israila take aiki shi ne ƙoƙarin magance yanayi mafi muni kafin ya zo, amma hakan ba lallai yayi musu amfani ba. Ba haka ake ƙulla ƙawance da sabuwar gwamnati ba.''