Mashahuran mutane, da lokuta da kuma abubuwa goma game da BBC
Shekara 100 da kafuwar BBC: Mashahuran mutane, da lokuta da kuma abubuwa goma game da BBC

Kafar yaɗa labaru ta British Broadcasting Corporation (BBC) na murnar cika shekara 100 da kafuwa.
Kafar yaɗa labarun, wadda ita ce mafi girma a duniya, an samar da ita ne a ranar 18 ga watan Oktoban 1922, a birnin London na kasar Ingila.
Tun daga wancan lokaci ta sha samun sauye-sauye masu ƙayatarwa.
Yayin da kafar take murnar cikar waɗannan shekaru, mun yi waiwaye kan wasu daga cikin lokuta masu muhimmanci, da lokuta masu ƙayatarwa da kuma mashahuran mutanen da suka kai BBC inda take a yanzu.
1. Tashar rediyon BBC ta farko

Bayan rufe gidajen rediyo da dama, BBC ta fara gabatar da shirye-shiryenta a kullum a ranar 14 ga watan Nuwamban 1922 a London na ƙasar Ingila.
Shiri na farko da aka gabatar da ƙarfe 06:00 na yamma, shi ne labarun duniya, wadanda aka tattaro daga kamfanonin dillancin labaru.
Daga nan sai hasashen yanayi, wanda hukumar lura da yanayi ta Birtaniya ta shirya.
Daraktan shirye-shiryen kafar, Arthur Burrows, ne ya gabatar, da harshen Ingilishi. Burrows ya karanta labaran ne sau biyu, na farko kuma ya karanta da sauri, sai kuma ya sake karantawa a hankali, yadda mutane za su iya rubuta abin da suka ji idan suna so.
2. Samar da sashen yaɗa labaru ga ƙasashen duniya

Asalin hoton, Getty Images
Ranar 19 ga watan Disambar 1932, sarki George V, ya gabatar da saƙonsa na kirsimeti ga al'ummar Birtaniya da na duniya.
A cikin saƙon nasa, wanda aka yaɗa ta mita mai ƙaramin zango ga masu amfani da turancin Ingilishi a ƙasashen da ke ƙarkashin masarautar Birtniya, ya bayyana tashar a matsayin wadda aka kafa domin amfanin "maza da mata, waɗanda dusar ƙankara, da rairayin hamada, da kuma tekuna suka nisanta su da juna, waɗanda ta hanyar iska ne kawai za su iya jin saƙonnin juna".
Da wannan jawabi ne aka bude tashar da ake kira 'BBC ta Daular Birtaniya (wadda yanzu ake kira Sashen BBC mai yaɗa labaru a kasashen duniya).

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu sashen yaɗa labarun BBC na ƙasashen duniya shi ne kafar yaɗa labaru mafi girma a duniya, ta ɓangaren harsuna da kuma masu sauraro.
Sashen na yaɗa labaru cikin harsuna 40 na faɗin duniya ta kafofin intanet, da talabijin, da kuma rediyo.
3. Makirfon BBC na tarihi.

A shekarun 1930 na'urar makirfo tana da matuƙar tsada, saboda haka ne BBC ta hada hannu da kamfanin Marconi wurin samar da nata makirfo din na kanta.
Inda a shekarar 1934 makirfon da aka kirkiro da ake ce wa Type A ya kawo sauyi a harkar yaɗa labaru.
An ƙirƙiro shi tare da inganta shi a tsawon shekaru, inda aka fi sanin shi da asalin makirfo na BBC, kamar yadda za a iya gani a wasannin kwaikwyo da fina-finan da BBC ta shirya.
4. Sashen Larabci shi ne na farko a cikin sassan BBC masu yaɗa labaru da harsunan ƙetare

Sashen Larabci na BBC ne ya zama na farko cikin harsunan waje da BBC ta fara amfani da shi wurin yaɗa labaru a shekarar 1938.
An ɗauko Ahmed Kamal Sourour Effendi, daga tashar yada labaru ta ƙasar Masar a matsayin mai gabatarwa.
Ɗaukan sa aiki ya sanya sashen ya samu karɓuwa nan take, kasancewar Effendi ɗaya ne daga cikin waɗanda aka fi ƙaunar muryarsu a ƙasashen Larabawa.

Asalin hoton, Getty Images
BBC ta ci gaba da ƙaddamar da sassan harsunan duniya daban-daban a shekarun da suka biyo baya, inda aka rinƙa ɓullo da shirye-shiryen rediyo da talabijin a faɗin duniya.
Shafin intanet na BBC kuwa an ƙaddamar da shi ne daga baya, a shekarar 1997, inda daga baya aka ƙaddamar da shafukan harsunan ƙetare.
Ƙaddamar da shafukan sada zumunta na BBC News da BBC World Service ne ya kawo lokacin da kafar ta faɗaɗa hanyoyin isar da labaru ga masu sauraron ta.
A yanzu, kafar BBC mai yaɗa labaru ga ƙasashen duniya na sauya alƙiblarta zuwa hanyar isar da labaru ta fasahar zamani.
5. Baƙar fata ta farko mai aikin haɗa shirye-shirye

Una Marson, ta kafa tarihi bayan ta zamo baƙar fata mai haɗa shirye-shirye ta farko a BBC.
Ƴar asalin Jamaica, Una ta kasance ƙwararriyar mai hada shirye-shirye kafin fara aiki a BBC a shekarar 1939.
Muƙaminta na farko shi ne mai taimaka wa mai haɗa shiri a ɗakin daukar shirye-shiryen talabijin na Alexandra Palace, amma ta zama cikakkiyar ma'aikaciyar BBC ne a watan Maris na 1941 a matsayin mai taimakawa wurin hada shirye-shirye a sashen "Empire Programmes".
Sha'awar da take da ita a ɓangaren rubutattun waƙoƙi ta taimaka mata wurin samar da 'Caribbean Voices', shirin da ke zuwa a kowanne mako ƙarƙashin shiri mai dogon zango na al'ummar tsibiran da ke kudancin nahiyar Amurka ta arewa.
6. Ƙarshen yakin duniya na biyu

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ranar ɗaya ga watan Mayu na shekarar 1945, BBC ta sanar da mutuwar Adolf Hitler.
Kwana ɗaya bayan haka, da ƙarfe 7 na yamma aka dakatar da shirye-shirye, inda aka sanar da cewa dakarun Jamus sun miƙa wuya a Italiya.
A ranar huɗu ga watan Mayu suka miƙa wuya a ƙasar Denmark.
Har tsawon kwanaki babu wanda ke da tabbas kan ko rikicin ya zo ƙarshe.
A ranar bakwai ga watan Mayu mutane suka yi dandazo a gaban fadar Buckingham, sai dai ba su samu labarin da suka yi shekara biyar suna tsammani ba.
Daga baya an gano cewa hakan ya faru ne saboda Birtaniya na jiran samun tabbacin cewa an murƙushe dakarun Nazi daga wurin sojoji Rasha da na Amurka.
Da karfe shida na yamma BBC ta shaida wa masu sauraronta cewar firaminista Churchill ba zai yi jawabi ba a wannan daren, amma da karfe 9:40 na dare aka dakatar da shirye-shirye, inda aka sanar cewar washe-gari za ta zamo ranar nasarar nahiyar Turai.
Washe-gari aka gabatar da jawabin Churchill, wanda al'umma suka zaƙu su ji, inda suke ta murna a kan tituna.
BBC ta ƙaddamar da shirye-shirye na musamman na kwanaki 10.
7. Gidan talabijin na BBC ya sada al'ummar duniya

A 1967 shirin talabijin na "Our World" ya kafa tarihi.
Kafin a gabatar da shi, shirye-shiryen talabijin da ake yaɗawa ta tauraron dan adam ya game wasu ƙasashe ne kawai a matsayin gwaji.
Misali, BBC ce kafar yada labaru ta farko da ta yada shirye-shirye masu inganci sosai a shekarar 1936.
To amma shirin "Our World" ya sha banban, kuma shirin ya yi koƙarin ƴadawa kai-tsaye, ƙasashen nahiyoyi daban-daban - karo na farko da ake ganin ƙasashen duniya a wuri guda ta hanyar tauraron dan adam.
A gudumawar da Birtaniya ta bayar ga shirin, tawagar mawaƙan da ake wa laƙabi da Beatles ta gabatar da shahararriyar waƙar nan mai taken 'All You Need is Love'.
Shirin ne ya ƙarfafa-gwiwar samar da wasu ƙayatattun shirye-shiryen talabijin a shekarun da suka biyo baya, waɗanda su ma suka haɗa ƙasashen duniya, ciki har da shirin Live Aid a 1985.

Asalin hoton, Getty Images
Taron mawaƙan wanda Bob Geldof da Midge Ure suka rinƙa shriyawa a wurare daban-daban an tsara shi ne domin neman tallafin kuɗin kai ɗauki ga al'ummar da yunwa ta shafa a Habasha.
BBC na daga cikin waɗanda suka sanya shirin ya yi nasara, kasancewar tana daga cikin kafafe talabijin mafiya girma a tarihi, inda take da masu kallo kimanin miliyan 400, a ƙasashe 60, waɗanda suka rinƙa kallo kai-tsaye.
8. Wata lema mai guba

Asalin hoton, International Spy Museum
Abin da ke cikin wannan hoton na sama an samar da shi ne a matsayin tamka, ta lemar da aka yi amfani da ita wajen kashe ma'aikacin BBC George Markov.
Ranar bakwai ga watan Satumban 1978, lokacin da Markov ke kan hanyarsa ta zuwa aiki a ginin BBC na Bush House da ke London, sai wani mutum da ba a san ko wane ne ba ya tokari bayan ƙafarsa da wata lema, daga nan kuma mutumin ya gudu.
Daga baya Markov ya fara rashin lafiya mai tsanani har ya kwanta a asibiti, inda ya shaida wa likitoci cewar yana da tabbacin cewa ma'aikatan tsaron cikin gida na Bulgaria (KGB) ne suka sanya masa guba.
Ya mutu bayan kwana uku yana da shekara 49, inda ya bar mata ɗaya da yarinya ɗaya mai shekara biyu.
Bayanan takardun ƴan sandan ciki sun bayyana wanda ya yi kisan da laƙabin "Piccadilly."
Sai dai babu wanda aka hukunta kan laifin kisan.
9. Kyautar gwarzon wasannin shekara na Afirka

Wannan ne kyautar da ake bayarwa kowacce shekara ga zakarun wasanni na nahiyar Afirka, wasu daga cikin waɗanda suka lashe kyautar a baya sun hada da ɗan wasan Liverpool Mohamed Salah ɗan asalin ƙasar Masar a shekarar 2018.
Daga shekarar 2001 an ware kyautar ce ga ƴan wasan kwallon ƙafa kawai, amma a shekra ta 2021 an sauya mata salo zuwa kyautar gwarazan wasanni na Afirka, domin haɗa sauran bangarorin wasanni.
10. David Attenborough da shirye-shiryensa na muhalli

Asalin hoton, Getty Images
Wannan ma'aikacin ɗan asalin Birtaniya kuma mai son abubuwan da suka shafi dazuka, ya yi suna game da shirin da ya rinƙa gabatarwa a BBC kan namun daji tsawon shekara 80, da kuma sansanyar muryarsa.
Miliyoyin mutane ne suka kalli wasu daga cikin shahararrun shirye-shiryensa kamar 'Blue Planet', da The Life Collection da kuma 'Natural World', kuma hakan ya taimaka masa wurin lashe kyautuka, har da na Emmys da kuma Baftas.
David ya fara gabatar da shirye-shirye ne a BBC a shekarun 1960, inda ya taka har matsayin babban jami'i, ya riƙe muƙamin shugaban tashar BBC Two da kuma daraktan shirye-shirye na BBC Television.
Aikinsa na ilimintar da mutane kan sauyin yanayi ya taimaka wajen ganin shirin kula da muhalli na Majalisar Dinkin Duniya ya zaɓe shi a matsayin zakaran kula da muhalli na 2021.
Shiri mai dogon zango da ya gabatar na baya-baya a BBC mai taken - The Green Planet - ya nuna yadda David ya shiga ƙungurmin dazukan ƙasashe masu yanayin zafi, zuwa dazukan yankunan ƙanƙara na arewacin duniya, domin nuna yadda tsirrai ke jure wa yanayi .











