Ya aka yi yara suka shiga rajistar zaɓe ta INEC a Najeriya duk da na'urorin tantancewa?

    • Marubuci, Nduka Orjinmo
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • An wallafa

Jim kaɗan bayan saka rajistar masu zaɓe ta latironi a Najeriya da aka yi kan shafin intanet, mutane suka fara hango matsaloli.

Masu bin diddigi a intanet sun gano katinan zaɓe masu yawa da ke ɗauke da hotunna yara. Wasu kuma sun yi rajistar fiye da sau ɗaya ta hanyar sauya yanayin fuskoki, ko tufafi, ko kuma zamansu.

Shekarun da doka ta tanda kafin mutum ya jefa su ne 18, kuma yi wa yara rajistar da kuma yin ta sama da ɗaya na nufin 'yan siyasa za su iya yin maguɗi.

Matsalolin a bayyane suke 'ƙarara'

Daga kallon katin zaɓen za a gane cewa katinan na ɗauke da hoton mutum ɗaya amma jami'an Inec ba su iya gane hakan ba.

"Abin a bayyana yake ƙarara ta yadda mutum ba ya buƙatar wata na'ura wajen gane yaran da shekarunsu ba su kai ba," a cewar Sunny Dada na cibiyar Institute for Media and Society da ke Legas.

Yanzu haka ana tuhumar ma'aikatan Inec 23 kan zargin hannunsu a gudanar da rajistar ta haramtacciyar hanya.

Ba abin mamaki ba ne a ga mutum ya zo da katin zaɓe na mamaci sakamakon ba a ɗaukar alƙaluman mutuwa a hukumance, amma ganin yara a rajistar da kuma masu yinta fiye da sau ɗaya suka jawo cecekuce da kuma fargaba.

Matsalolin da aka saba gani a baya sun ƙara fitowa fili bayan ƙaddamar rajistar latironi.

A baya, a takardu kawai ake iya samun rajistar waɗanda ake kafewa a jikin bango a rumfunan kaɗa ƙuri'a.

Yanzu kuwa rajistar ta latironi da ake wallafawa a intanet na bai wa kowa da kowa damar tsettsefe sunayen da ke cikinta na mutum miliyan 93.5 na masu kaɗa ƙuri'ar a ƙasa baki daya.

Wasu masana harkokin intanet sun rungumi ƙalubalen gano matsaloli a bayanan masu yawan gaske, har ma suka ƙirƙiri manhajoji don yin hakan.

Wani mai bincike a intanet ya faɗa a Twitter cewa sun gano dubban mutanen da suka yi rajistar fiye da ɗaya, wani kuma ya bayyana wata manhaja da ke hasashen shekarun haihuwa da za su tantance yara daga rajistar.

Ɗan jarida Jaafar Jaafar kuma ya zaɓi hanya mafi wuya, inda ya dinga bin dubban sunayen ɗaya bayan ɗaya da kuma fuskokinsu a kan rajistar.

"Duk rajistar da ke ɗauke da hoton mutum a gicciye ko kuma hoton da yake dariya to akwai alamar tambaya a kansa a wajena," kamar yadda ya shaida wa BBC.

Wasu daga cikin waɗanda ba su kai shekaraun zaɓe da ke cikin rajistar sun yi ta ne tun daga 2011, a cewarsa.

Ana ganin cewa kafe rajistar ta gwaji ko kuma wucin-gadi da Inec ta yi alama ce ta kwatanta adalci wadda ke aiki yayin da doka ta tanadi cewa hukumar ta saurari duk ƙorafin da aka yi game da sunayen.

Hukumar ta ce tana maraba da "tallafin" da 'yan Najeriya za su ba ta wajen tantance rajistar kuma ta ce za ta kafe ingantacciyar rajistar kafin ranar 25 ga watan Fabariru - ranar fara kaɗa ƙuri'a.

Sai dai bayan ta saki sunayen na gwaji a watan Nuwamba, ta ce ta riga ta tantance sunayen wata uku bayan kammala aikin rajistar a ƙasa baki ɗaya.

Shaci-faɗi

Inec ta ce ta gano tare da soke rajista miliyan 2.7 da ba su dace ba, amma duk da haka rajistar yara da masu kati da yawa sun tsallake.

Sakamakon haka ne mutane da dama suka nuna damuwa game da yadda ɗaiɗaikun mutane suka gano irin waɗannan matsaloli, abin da ya jawo wasu suka fara yin shaci-faɗi.

Wasu da yawa sun yi imanin cewa Inec ta fi soke rajistar mutane daga kudancin ƙasar. Misali, a Jihar Bayelsa an soke kashi kusan 70 cikin 100 na sababbin masu rajistar saboda rashin daidaito a bayanai.

Amma fa an gano cewa akwai yara da kuma rajistar mutum fiye da ɗaya a faɗin Najeriya, ciki har da jihohin Kudu.

"Abu ne da ya shafi ƙasa baki ɗaya, akwai abubuwa da yawa game da rajistar nan," a cewar Jaafar ɗan asalin Jihar Kano, yana mai cewa ɗaya daga cikin abubuwan da ya sa a gaba shi ne ƙaryata irin waɗannan shaci-faɗin.

Mutane da yawa kamar Mista Dada, na nuna damuwa kan waɗannan matsaloli yayin da 'yan watanni suka rage kafin babban zaɓen, amma Shugaban Inec Farfesa Mahmood Yakubu ya tabbatar wa 'yan Najeriya babu wani mai ƙarancin shekaru da za a bari ya kaɗa ƙuri'a.

Najeriya ta fuskanci matsaloli da yawa game da zaɓuka a baya, amma ana ganin fara amfani da na'urorin zamani zai sauƙaƙa lamura duk da cewa akwai ƙalubala.

Mutum fiye da miliyan bakwai da suka cike fom ɗin rajistar a intanet tun da farko kafin rufe shafin a watan Yuli ba su iya zuwa sun yi rajistar ba a ofisoshin Inec saboda ƙarancin ma'aikata da na na'urorin gudanar da aikin.

Kazalika, miliyoyin masu rajistar ba su karɓi katin da zai ba su damar kaɗa ƙuri'ar ba, duk da cewa Inec ta tabbatar musu za a kammala aikinsu zuwa tsakiyar Disamba.

Wannan ne karon farko da za a yaɗa sakamakon zaɓen shugaban ƙasa kai-tsaye ta inatanet ta hanyar amfani da fasahar da masu sa ido suka yaba sosai bayan gwada ta a wasu zaɓukan gwamna a jihohin Ekiti da Osun da Anambra.

Na'urar tantance masu kaɗa ƙuri'a a ranar zaɓe ta Bimodal Voter Accreditation System (Bvas) na amfani da bayanai kamar zanen yatsu da Inec ta ɗauka a lokacin rajista don tabbatar da cewa sai wanda ya cancanta ne zai kaɗa ƙuri'a.

An yi imanin cewa ba za ta bari a yi maguɗi a zaɓe cikin sauƙi ba, kuma duk da nuna rashin amincewa game da amfani da ita musamman daga 'yan APC mai mulki - wadda ta ce babu tabbas ko za ta yi aiki a yankunan karkara, Inec ta ce babu gudu babu ja da baya.