Iyalan Glazer ba su damu da Man United ba - Ronaldo

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan Manchester United, Cristiano Ronaldo ya ce Iyalan Glazer ba kungiyar ce a gabansu ba a fannin wasanni.
A wata hira da aka yi da Ronaldo a Talk TV ya ce an yaudare shi a kungiyar, ya kuma fadi batutuwa da dama kan United.
"Manchester kungiyar 'yan kasuwa ce - suna samun kudi daga kasuwanci," in ji Ronaldo said.
"Zai yi wahala Manchester ta koma kan ganiya a harkar kwallon kafa nan da kaka biyu ko uku masu zuwa."
Kyaftin din Portugal, mai shekara 37, wanda ya ci kwallo daya a kakar nan ya ce ''Masu kungiyar ba su damu da ci gaban kungiyar ta fannin wasanni ba.''
Dan wasan ya kara da cewar bai taba haduwa da iyalan Glazer ba, wadanda suka mallaki kungiyar a 2005.
United ta fitar da jawabin cewar tana duba yiwuwar mayar wa da Ronaldo martani, amma tana tattara shaida kan dangantaka tsakaninta da dan kwallon.
Amma yanzu ta mayar da hankali kan tsara shirye-shiryen da za ta gabatar da zarar an koma ci gaba da buga gasar Premier League, bayan gasar kofin duniya.
Manchester United ba ta kara daukar wani babban kofi ba tun bayan Europa League a 2017 - karo da dama magoya baya sun yi zanga-zanga kan yadda iyalan Glazer ke gudanar da kungiyar.
''Magoya baya na kan gaskiya,'' in ji Ronaldo. ''Ya kamata su san gaskiya. 'Yan wasa na son ganin kungiyar a kan kololuwa haka ni kaina. Dalilin da ya sa na sake komawa kungiyar. Ina son Manchester United.
''Akwai wani abu a kungiyar da baya taimakawa Manchester United ta koma kan ganiya, kamar yadda Manchester City da Liverpool da yadda Arsenal ke a wannan lokacin''.











