Camavinga ya tsawaita kwantiraginsa a Madrid

Eduardo Camavinga

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Real Madrid ta amince da sabuwar yarjejeniya da Eduardo Camavinga domin ci gaba da rike dan wasan na Faransa a kungiyar har zuwa shekarar 2029.

An ruwaito cewa dan wasan mai shekaru 20, wanda ya koma kungiyar ta La Liga daga Rennes yana da shekaru 18 a watan Agustan 2021, ya amince da kwantiragi mai sharadin tafiya naYuro biliyan daya.

Camavinga ya buga wa Real wasanni 114, inda ya fara a wasanni takwas daga cikin 12 da kungiyar ta buga a bana.

Ya lashe kofuna shida a kakar wasanninsa biyu na farko a Sifaniya, ciki har da gasar zakarun Turai a 2021-22.

Abokan wasansa Rodrygo da Vinicius Junior su ma kwanan nan sun kulla sabuwar yarjejeniya ta dogon lokaci a Real Madrid.

Camavinga ya zama matashin dan wasan Faransa mai karancin shekaru cikin shekaru 106 a watan Satumbar 2020, inda ya fara buga wasansa na farko a gasar Uefa Nations League da Croatia yana da shekara 17 da wata tara.

Ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru shida a Bernabeu bayan da ya koma kungiyar daga Ligue 1 kan fam miliyan 27, inda da farko ya daure shi a kungiyar har zuwa shekarar 2027.