Zaben Amurka : Republican ta kama hanyar kwace Majalisar Wakilai

An wallafa

Sakamakon zaben tsakiyar wa'adi na Amurka na nuna alamun cewa 'yan jam'iyyar Republican masu ra'ayin rikau na kan hanyarsu ta karbe iko da majalisar wakilan kasar, abin da ake ganin wata babbar mahangurba ce ga Shugaba Biden.

Yayin da ya rage a samu sakamakon jihohin Alaska da Hawaii, kafar labarai ta CBS ta Amurkar ta nuna cewa 'yan Republican sun samu kujeru 198, yayin da 'yan Democrat suka tsira da 180.

Gwagwarmayar wadda za ta kama iko da majalisar dattawa kuwa ta dogara ne ga wasu muhimman kujeru  a Georgia, da Pennsylvania da Arizona da kuma Nevada.

Kubucewar daya daga cikin majalisun dokokin na Amurka, daga 'yan Democrat, za ta bai wa 'yan Republican damar taka burki ga manufofin Shugaba Biden, na Democrat.

A Florida gwamnan jihar dan Repulican Ron DeSantis ya kara yawan tazarar da ya bayar a nasarar da ya samu a 2018.

Ana hasashen zai yi wa abokin hamayyarsa na Democrat fintinkau da sama da kashi 15 cikin dari. Mr Rubio ya ce jamiyyar Republican na ganin haske.

Ya ce, 'ina jin karin karfi da farin cikin aiki a majalisar dattawa fiye da a ko wane lokaci, saboda na yi amanna muna kan hanyar samun sabon shugabanci.

Ana ganin wannan sakamako mai rinjaye da ya samu zai haifar da hasashe cewa kila ya nemi takarar shugaban kasar a 2024 - kila ke nan ya yi gogayya da tsohon shugaba Donald Trump, wajen samun tutar jam'iyyarsu ta Republican.

A fafatawar neman kujerar majalisar dattawa ta Florida, dan Republican da ke kai, Marco Rubio, a tsanaki ya tsira da kujerarsa, inda ake ganin zai samu kusan kashi 56 cikin dari na kuria.

A jihar Massachusetts, Maura Healey ta zama ta farko da aka zaba a matsayin gwamnar jiha, da ke bayyana kanta karara cewa 'yar neman jinsi daya ce.

Can a Maryland kuwa dan Democrat Wes Moore ya zama bakar fata na farko gwamna.