Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'An taɓa tofa min yawu a fuska saboda ni baƙa ce'
- Marubuci, Ashley Lime
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC 100 Women
- An wallafa
Mai sana'ar neman 'yan ƙwallon kwando Sarah Chan ta zagaya faɗin duniya, daga Sudan zuwa Kenya, zuwa Turai da Amurka - amma sai da ta fuskanci yaƙi, da wariyar launin fata, da cin zarafi na jinsi kafin a kan hanyarta.
"An taɓa tofa min yawu a fuska kawai saboda ni baƙa ce," a cewar tsohuwar 'yar ƙwallon kwandon.
"Na fuskanci wariyar launin fata ta hanyoyi da yawa fiye da yadda nake tsammani."
Yanzu, a matsayinta na mace ta farko da ke jagorantar tawagar neman 'yan ƙwallo na gasar NBA - gasar ƙwallon kwando mafi girma a duniya - Ms Chan na ƙarfafa wa masu tasowa gwiwa don su yi amfani da damarmaki a ɓangaren wasanni.
"Ƙwallon kwando ce ta kai ni inda nake a yanzu. Ita ce komai da komai a wajena," in ji matar, wadda ke cikin Jerin Mata 100 na BBC saboda ƙarfafa wa mata gwiwa a shekarar nan.
Ita da danginta sun zauna a birnin Khartoum na Sudan lokacin yaƙin basasar ƙasar na biyu. An sha yunƙurin sace mahaifinta, kuma tana iya tuna yadda aka dinga tashin ta tsakar dare daga barci sakamakon hayaniya a kusa da gidansu.
Daga baya sun gudu da zimmar neman rayuwa mafi zaman lafiya da kuma ilimi a Kenya.
"Shi ne wuri na farko da muke ganin za mu samu 'yancin yin wasanni, saboda a Sudan haramun ne a ga mace da gajeren wando ko kuma tana buga wasa," a cewar Ms Chan.
A can ne kuma sha'awarta ta ƙwallon kwando ta bayyana. Ta bayyana tattaunawar da ta sa ita da 'yar uwarta suka fara buga wasa a karon farko. "Ina iya tunawa cewa ina cikin yaran da suka fi tsayi a makaranta a Kenya, sai shugaban makarantar ya nemi mu fara buga wasa.
"Gaskiya a lokacin ba na tunanin hakan. Na ce masa ya yi haƙuri ba zan yi ba - kuma saboda haka nan take ya mayar da wasannin tilas."
Bayan shafe shekara tana samun horo, ta samu tallafin karatu na ƙwallon kwando a Jami'ar Union a Jackson, Tennessee, da ke Amurka. Bayan shafe shekara 14 tana wasa, ta yi wasannin gasa a Turai da Afirka.
"Mutum kan taimaka wa mutane da yawa ta hanyar ƙwallon kwando. Ƙwallon kan sauya rayuwar mutane," a cewarta.
Amma Ms Chan ta fuskanci wariya a ɓangaren wasanni - ciki har da wani lamari da ya faru a cewarta lokacin da ta yi balaguro zuwa Aljeriya tare da abokan wasanta, inda wani mutum ya tofa mata yawu a fuska.
"Ba don tarbiyyar da iyayena suka ba ni ba, ba zan iya jure hakan ba," kamar yadda ta bayyana.
"Kafin na bar gida, mahaifina da mahaifiyata sun faɗa min, 'Ke me kyau a yadda kike.'"
"Idan mutum ya shekara 18 dole ya fara neman abokin zama," in ji ta. Akan matsa wa 'yan mata su zaɓi ko dai su zauna a makaranta "ko kuma su nemi taimakon kuɗi daga mutumin da iyayensu za su zaɓa musu", a cewar bayaninta.
"Na yi ta kuka tsawon lokaci.
"Har sai da ta kai na daina kukan kuma na fara tunanin abin da zan yi don na kawo gyara."
Ta haka ne Ms Chan ta ƙaddamar da gidauniyar Home At Home/Apediet Foundation, wata ƙungiya da ke yaƙi da auren wuri da kuma neman 'yancin ilimi da wasanni.
Ta ce tana ɗaukar aikin taimakon da take yi da muhimmanci, "saboda mutane sun ga wani abu a wajena da ni ban gani ba".
Ta irin wannan hanyar ce ta samu aiki da kulob ɗin Toronto Raptors, bayan wani shugaba a hukumar NBA ya gan ta tana aiki a wani sansanin ƙwallon ƙafa a Kenya.
Yanzu da yake tana aiki da ƙungiyar da aka kafa a 1995 a ɓangaren NBA na ƙasar Kanada, aikin Ms Chan shi ne ta gano haziƙan 'yan ƙwallo da ke tasowa - maza da mata - don ta tallafa musu da kuma sama musu ƙungiyoyin ƙwallon kwando a Kudan Amurka.
A kwanan nan, ta yi balaguro zuwa Uganda da Tanzania don ɗaukar 'yan wasan da za su buga babbar gasa a Rwanda a shekara mai zuwa.
"Ina fatan abin zai kai ga samun gasar mata ta WBAL ta Afirka," a cewarta. "Wannan ne fatana ga 'yan matan nan, a ce al'ada ba ta daƙile su ko kuma wani tunani.
"Sun samu 'yanci a zukatansu kuma za su iya cimma burikansu a matsayinsu na 'yan Adam, ba wai wani abu ya daƙile su ba saboda jinsinsu."