Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Gangar da mata kadai ke buga ta a Nijar 'da ke warkar da maras lafiya'
Gangar da mata kadai ke buga ta a Nijar 'da ke warkar da maras lafiya'
An wallafa
Ku danna hoton da ke sama don kallon bidiyon:
A cikin al'ummar Abzinawa ta Nijar, mata na buga wata ganga da aka yi ta da fatar akuya, wacce ake kira tendé.
Ƴaƴa kan gaji iyayensu wajen iya buga gangar da rera waƙoƙin da ake yi yayin buga ta don kar al'adar ta gushe.
Akan buga gangar ne a yayin bikin hawan raƙuma sannan wasu lokutan akan kada wa maras lafiya, inda nan da nan yake samun sauƙi kamar yadda al'ummar suka yi amanna.
Maza ba sa buga gangar saboda ana so su kasance masu kamun kai da martaba.