Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Harin da aka kai ɗakin jarrabawa a Afghanistan ya hallaka mutum 19
'Yan sanda a birnin Kabul sun ce harin kunar bakin wake da aka kai wata cibiyar rubuta jarrabawa ya hallaka mutum 19, wasu da dama kuma sun jikkata.
Lamarin ya faru ne a cibiyar ilimi ta Kaaj da ke gundumar Dasht-e-Barchi a wajen birnin.
Jami'an tsaro sun ce, dalibai na gwajin jarabawar shiga jami'a a lokacin da lamarin ya faru.
Yawancin mazauna yankin 'yan kabilar Hazara marasa rinjaye ne da ake yawan kai wa hare-hare.
Hotunan da gidan talbijin din yankin ya nuna, da kuma aka yada a shafukan sada zumunta, ya nuna yadda gawawwaki zube akasa a wani asibiti da ke kusa.
Wata kafar yada labaran da ke kusa da cibiyar ilimin mai zaman kanta, ta nuna baraguzan gini da teburan da suka jirkice a cikin ajujuwa.
"Ba mu gan ta anan ba," in ji wata mata da ta zo neman 'yar uwarta a daya daga cikin asibitocin da aka kai wadanda harin ya shafa, ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa shekarar kanwarta 19.
Amurka ta yi Allah-wadai
Amurka dai ta yi Allah-wadai da harin, da ta ce an kai wa daliban da ke kokarin zana jarrabawa, kuma babban abin kunya ne.
Amurkar ta ce daliban su na da 'yancin samun ingantaccen ilimi cikin kwanciyar hankali ba tare da tsoro ba, kamar yadda wakilin kasar a Afghanistan, Karen Decker, ta wallafa a shafinta na tiwita.
A nata bangaren Taliban ta ce tana kokarin dawo da doka da oda.
Sai dai masu da'awar jihadi na kungiyar IS sun ci gaba da kai hare-hare.
An dade ana kai hare-hare makarantu da asibitocin da ke yankin Dasht-e-Barchi tun kafin Taliban ta karbe iko, ko a bara an kai harin da ya hallaka akalla mutum 85 a wata makarantar 'yan mata.
Cibiyar lafiya ta Kaaj dai mai zaman kanta ce, wadda ke koyar da dalibai maza da mata.
Yawancin makarantun mata da ke Afghanistan a rufe suke, tun bayan Taliban ta karbe ikon kasar a watran Agustan bara, sai dai yawancin makarantu masu zaman kansu sun sake budewa.
Sai dai dama can kabilar Hazarat da yawancinsu musulmai ne na mazahabar Shi'a sun ji ma su na fuskantar hare-hare daga 'yan Taliban da IS, wanda dukkansu 'yan Sunni ne.
Kabilar Hazarat su ne na uku mafi girma a Afghanistan.
A yau Juma'a, ministan harkokin cikin gida a gwamnaytin Taliban, ya ce jami'an tsaro na inda aka kai harin.
Yankin Dasht-e-Barchi aya jima yana fuskantar hare-hare, ko a bara an kai hari wata makarantar 'yan mata da dalibai 85 suka mutu, wasu daruruwa suka jikkata.