Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shin ko Barcelona za ta kara bai wa Real tazarar maki a La Liga?
Getafe ta ziyarci Barcelona domin buga wasan mako na 18 a gasar La Liga da za su fafata ranar Lahadi a Nou Camp.
Barcelona wadda ta yi wasa 16 tana matakin farko a kan teburi da maki 41 da tazarar maki uku tsakaninta da Real Madrid ta biyu.
A ranar ta Lahadi a dai karawar mako na 18 a babbar gasar tamaula ta Sifaniya, Real Madrid ta zaiyarci Athletic Bilbao.
Ita kuwa Getafe tana ta 16 a kasan teburi mai maki 17.
A cikin watan nan na Janairu, Barcelona ta dauki Spanish Super Cup a Saudi Arabia, bayan da ta ci Real Madrid 3-1.
Kofin farko da Xabi ya dauka a kungiyar a matakin kociyan Barcelona.
Tuni kociyan Barcelona, Xavi Hernández ya sanar da 'yan wasan da zai fuskanci Getafe ranar Lahadi.
Ter Stegen, Bellerín, R. Araujo, Sergio, O. Dembélé, Pedri, Ansu Fati, Iñaki Peña, Christensen, Marcos A da kuma Jordi Alba.
Sauran sun hada da Kessie, S. Roberto, F. De Jong, Raphinha, Kounde, Eric, Balde, Gavi, Pablo Torre, Arnau Tenas da kuma A. Alarcón.